Kashi na 05 – Sarki Ludwig yana da rai

Now live
mintuna 15:00
28.09.2012

Radio D (1) - Lektion 5: König Ludwig lebt

Paula da Ayhan sun yi wa sabon abokin aikinsu maraba da shiga Radio D. Da ma suna da wani aiki na gaggawa: Ana rade-radin marigayi Sarki Ludwig na Bavaria yana da rai, don haka suna son su bincika.

Pilipp ya hadu da sababbin abokan aikinsa, da Paula da Ayhan, ya kuma hadu da miskilar maikula ofis dinsu, Josefine. Lokaci ya kure musu, tun da tuni Philipp da Ayhan sun samo aikinsu na farko. Ana rade-radin cewa shahararren Sarkin nan na Bavaria, Sarki Ludwig II, na nan da ransa, duk da zaton da ake masa ya mutu, ta wani yanayi mai ban mamaki a 1886. 'Yan jaridar sun tafi Fadar Neuschwanstein don su bincika labarin, su kuma gane wa idonsu.