1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasuwanci tsakanin Jamus da Afirka

Usman Shehu Usman
June 15, 2018

Kamfanoni da 'yan kasuwar Jamus sun bude kawancen huldar kasuwanci mai karfi da kasashen Afirka domin habaka tattalin arziki a tsakanin nahiyoyin biyu.

https://p.dw.com/p/2zet3
Deutschland Presseschau Horst Köhler zurückgetreten
Wasu daga cikin jaridun JamusHoto: AP

Kyakkawar fata ga ‘yan kasuwar Jamus da ke son zuba jari a Afirka, shi ne sharhin jaridar Handelsblatt. inda ta ruwaito ma'aikatar tattalin arzikin na cewa yanzu kamfanonin Jamus na da kwarin gwiwa bisa kasuwanci a Afirka, jaridar ta kara da cewa yanzu haka kasashen biyar da Jamusawa suka fara zuba jari gada-gadan su ne Kudivowa, Senegal, Habasha, Ghana da kuma Ruwanda.

ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba matsalar yunwa da talauci da ke addabar al'ummar Afirka ta Kudu, inda ta yi misali da wata mata mai suna Patricia, wace yanzu haka ta koma bakin da ji a kusa da birnin Cape Town, Patricia ta bayyana wa jaridar irin talauci da mutane irin ta suke fuskanta, yayinda tattalin arzikin kasar Afirka takludu ya tabarbare. A lokacin mulkin tsohon sjhugaban kasar Jacob Zuma, tattalin arzikin kasar Afirka ta kudu ya yi rauni matuka.
Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta duba ci gaban siyasa da aka samu a kasar Habasha. A cewar jaridar sabon firaministan kasar Abiy Ahmed na baiwa duniya mamaki bisa sauye sauyen da yake kawo wa a fannin siyasa. Misali a jihar Oromia kadai an saki fursunonin siyasa kimanin dubu 40,000 Jaridar ta ce guguwar sauyin a kasar Habsha wace Firaminista Ahmed ya kawo ba ta tsaya kan sasantawa da 'yan adawar kasar kadai ba, ya ma bayyana kawo karshen gaba da ke tsakanin kasarsa da makobciyarsu Eriteriya.

Äthiopien Premierminister Dr. Abiy Ahmed
Shugaban kasar Habasha Abiy AhmedHoto: Oromia Government Communication Affairs Bureau

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi bincike ne inda ta ce, daga cikin masu horar da 'yan wasa da suka samu halartar gasar cin kofin duniya akwai Jamusawa biyu, wato baya ga Joachim Löw mai horar da 'yan wasan Jamus, akwai kuma Gernot Rohr, wanda ya kai ga yin nasarar samar wa Najeriya tikitin zuwa kasar Rasha a gasar ta bana. Jaridar ta duba tarihin wannan mai horar da 'yan wasan na Najeriya Super Eagles Gernot Rohr mai shekaru 64, da ya yi fice a kulub din Bayern Munich, daga 1977. Jaridar ta ce Gernot Rohr ba bako bane a Afirka, kafin Najeriya ya horar da 'yan wasan kasar Gabon da na Jamhuriyar Nijar da kuma Burkina Faso.