1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsina: Bunkasa harkar noman rani

February 27, 2019

Wani matashi a Katsina da ya kammala karatun jami'an babu aikin yi, ya kama sana'ar noman rani dan dogaro da kansa. Yanzu haka matashin ya yi shuke-shuke kala-kala na kayan lambu wanda har ya fara deba yana sayarwa.

https://p.dw.com/p/3EBX7
Wannan wani tsohon hoto ne na masu aikin noma a Katsina muka yi amfani da shi
Wannan wani tsohon hoto ne na masu aikin noma a Katsina muka yi amfani da shiHoto: AP

Wannan matashi dai ya ce bayan ya kammala karatu ya ga cewar babu abin da ya kamata ya yi  shi ne ya kama dogaro da kansa, matashin mai sunan Abdullahi Bature ya ce, ya yanke shawarar kama sana'ar noman rani dan amfani kansa da sauran al'umma: "Babban abin da ya sa na kama noman rani shi ne bayan na kammala karatuna na ga ya kamata na kama wata sana'a wadda zan dogara da kaina saboda na lura dogaro ga gwamnati ba biyan bukata." Wannan matashi dai ya kwashe kusan shekaru biyar yana wannan sana'a ta noman rani a katsina.