1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Keita da Cisse za su je zagaye na biyu a zaben kasar Mali

August 2, 2013

Sakamakon zaben Mali na nuni da cewar za a je zagaye na biyu a ranar 11 ga watan Augusta, a yayin da a Zimbabwe aka fara sanar sakamakon zaben 'yan majalisa.

https://p.dw.com/p/19J6A
Artikel: Mali geht in die Stichwahl für den 2. August 2013 Ein Anhänger von Soumaila Cissé jubelt über den Einzug in die Stichwahl Schlagworte: Soumaila Cissé, Mali, Wahlen, Stichwahl Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 2. August 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Bamako, Mali
Hoto: DW/K.Gänsler

Sakamakon zaben shugaban kasar Mali na nuni da cewar tsohon fraiministan Ibrahima Boubacar Keita, ya zo na farko da mafi yawan kuri'u, sai dai zai kara da tsohon ministan kudi Soumaila Cisse a zagaye na biyu, kasancewar bai samu adadin kuri'un da zasu bashi damar lashe zaben kai tsaye ba.

Sakamakon da hukumomin kasar suka gabatar a wannan Juma'ar dai na nuni da cewa, Keita ya samu kashi 39.24 bisa 100 na yawn kuri'un da aka kada a zaben da ya gudana ranar 28 ga watan Yuli, a yayin da Cisse ya samu kashi 19.44, kana dan takarar Adema, jam'iyya mafi girma a Mali, kuma tsohon direktan harkokin hakar ma'adinai, Dramane Dembele, ya samu kashi 9.59 daga cikin 100.

Ministan harkokin cikin gida na Mali Moussa Sinko Coulibaly wanda ya gabatar da sanarwar, ya ce wajibi ne kotun tsarin mulkin kasar ta tzabbatar da kwarya-kwaryar sakamakon, kafin a gudanar da zagaye na biyun zaben shugaban kasar ta Mali a ranar 11 ga watan Augusta.

Ya ce "kuri'un da kowane dan takara ya samu da kuma kason da ya samu, kamar yadda takadar da kotun tsarin mulki ta bayyana, dan takara Soumaila Cisse, ya samu kuri'u 605.901, dan takara Ibrahima Boubacar Keita ya samu kuri'u milliyon daya da dubu biyu da dari shida da hamsim da bakwai".

Ibrahim Boubacar Keita Presidential candidate Ibrahim Boubacar Keita speaks at a campaign rally in Bamako July 21, 2013. Mali is due to hold presidential elections on July 28. REUTERS/Joe Penney (MALI - Tags: ELECTIONS POLITICS)
Ibrahim Boubacar KeitaHoto: Reuters/Joe Penney

Sanarwar tafiya zagaye na biyun zaben shugaban kasar dai zai taimaka wajen kwantar da hankulan al'ummar Malin, bayan tayar da jijiyar wuya da suka yi bisa ga sakamakon farko da ya nuna cewar dan taka Keita ne ya doshi lashe zaben kai tsaye a zagayen farko. Cisse dai ya bayyana cewar ba zai amince da sakamakon ba, idan har ba za'a je zagaye na biyu ba.

A wannan juma'ar dai magoya bayan Keita da Cisse sun bazu a titunan birnin Bamako suna wake wake da kade kaden murnar sanarwar sakamakon.

Babban sakataren reshen matasa na jam'iyyar Keita Abdoulaye Magassouba ya ce, a shirye suke a fafata a zagaye na biyun zaben shugaban kasar.

Duk da cewar su ma suna bukukuwan murna, 'yan jam'iyyar Cisse ta URD, sun nuna shakku. Shugaban reshen matasa na jam'iyyar Madou Diallo ya fada wa manema labaru cewar, suna zargin almundahana da magudi a bangaren Keita da ma'aikatar harkokin cikin gida. Ko da yake suna murna da zuwa zagaye na biyu...

Ya ce "a yanzu mu za mu yi shirin zuwa zagaya na biyu a cikin babbar manufa, mu kasance masu kishin demokaradiyya, sai dai mu ce Allah ya ba mai rabo sa'a domin ci gaban kasar Mali".

Shi kuwa dan takara Dembele ya yi amfani da diplomasiyya wajen cewar, ya amince da sakamakon zaben, tare da kira ga magoya bayansa da su yi hakuri da shi.

Titel: DW_Soumaila-Cisse1 und 2 Schlagworte: Bamako, Präsidentschaftswahl, Spitzenkandidat, Staatsstreich, Soumaïla Cissé, URD (Union pour la République et la Démocratie, Union für Republik und Demokratie) Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 29. Juli 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Bamako, Mali
Soumaila CisseHoto: DW/K.Gänsler

Wannan kasa mai fama da talauci a yankin yammacin Afirka dai, na kokarin farfadowa daga juyin mulki da sojoji suka yi, a hannu guda kuma da somamen 'yan tawaye, wanda ya sanya Faransa tura dakarunta zuwa wannan kasa da ta yiwa mulkin mallaka a baya.

Mutane 27 ne dai suka yi takara a zaben shugaban kasar ta Mali wanda ya gudana a ranar 28 ga watan Yulin da ya gabata. Kashi 51.5 daga cikin al'ummar Mali miliyan shida da rabi ne dai suka kada kuri'unsu a cewar ministan harkokin cikin gida Kanal Sinko Moussa Coulibaly.

Mai shekaru 68 da haihuwa, mutumin da ya sha kaye a takararsa sau biyu, Keita ya yi yakin neman zabenshi ne a wannan karon bisa akidar daukaka Mali, bisa rarrabuwar kasar sakamakon rigingimun da yankin arewaci ya fuskanta daga 'yan kabilar Abzinawa da masu tsananin kishin addini.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal