1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya na girbe abin da ta shuka

September 23, 2013

Kungiyar al-Shabab ta Somaliya, ta ce ita ke da alhakin kai hari a cibiyar kasuwancin Kenya, bisa taimakon da Kenya ta baiwa Somaliya wajen fatattakarsu.

https://p.dw.com/p/19mjN
Hoto: Reuters

Ana ci gaba da musayar wuta a rana ta uku tsakanin jami'an tsaro da kuma 'yan kungiyar al-Shabab da suka yi garkuwa da wasu mutane da dama a wata cibiyar kasuwanci dake kasar Kenya. Ya zuwa yanzu dai hayaki na ci gaba da tashi daga cikin shagon inda ake ci gaba da jin karar tashin bindiga da kuma abubuwa masu fahsewa.

Jami'an tsaron kasar ta Kenya sun yiwa cibiyar kasuwancin kawanya, inda rahotanni ke nuni da cewa ya zuwa yanzu sun toshe duk wata kafa da 'yan ta'addan ka iya tserewa daga ginin cibiyar, da suka yi garkuwa da mutane masu yawa a ciki.

Nairobi Unruhen Schießerei
Jami'an tsaron kasar Kenya na kokarin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.Hoto: AP

Rahotanni sun bayyana cewa ya zuwa yanzu mutane sama da 60 ne suka rasa rayukansu sakamakon musayar wutar da ake tsakanin jami'an tsaro da kuma 'yan tawayen, a harin da kungiyar al-Shabab ta Somaliya dake da alaka da kungiyar al-Qa'ida ta dauki alhakin kaiwa.

Rundunar 'yan sandan kasar ta Kenya ta bayyana cewa kawo yanzu ta cafke sama da mutane 10 da take tuhuma da hannu cikin harin da aka kai a cibiyar kasuwancin mai suna Westgate Shopping Mall, yayin da ma'aikatar tsaron kasar ta sanar da cewa sun samu nasarar kashe mutane uku daga cikin maharan inda wasu kuma suka samu raunuka.

Gwamnati na kwantar wa da al'ummar kasar hankali.

A hannu guda kuma Ministan harkokin cikin gida na kasar ta Kenya Joseph Ole Lenku, ya tabbatarwa da 'yan kasar cewa jami'an tsaro sun karbe iko da ginin cibiyar kasuwancin, tare kuma da bukatar, su kwantar da hankulansu.

" Muna so mu tabbatarwa da al'ummar Kenya cewa, jami'an tsaronmu suke da cikakken iko da gurin, kuma ba tare da bata lokaci ba za'a kawo karshen barin wutar da ake yi. Kokarin da ake na tserar da wadanda aka yi garkuwar da su shima ya na tafiya yadda ya kamata, kuma muna da tabbacin cewa mutanen da aka yi garkuwar da su kalilan ne suka rage a cikin ginin yanzu".

Sai dai kuma al'ummar kasar na ci gaba da nuna damuwa kan yadda jami'an tsaro suka kasa shawo kan matsalar cikin gaggawa. Wani mai bincike kan al'amuran tsaro a jami'ar nazarin harkokin tsaro dake Nairobin kasar Kenyan, Emmanuel Kisiangani, yace hakan na faruwa ne saboda a kwai mutane da dama da aka yi garkuwa da su.

Nairobi Kenia Afrika Schießerei Amoklauf Einkaufszentrum
'Yan kasar Kenya na kokarin tsira da ransu bayan da aka yi garkuwa da wasu mutane a wata cibiyar kasuwanci.Hoto: Reuters

"Saboda a kwai mutanen da ba suji, basu gani ba a cikin ginin, a kwai yiwuwar idan aka matsa da bude wuta za'a iya kashe wadannan mutane fararen hula da aka yi garkuwa da su".

Kasashen dake makwabtaka da Kenya sun daura damara

Kasashen dake makwabtaka da kasar ta Kenya dai tuni suka fara abin nan da ake cewa "idan gemun dan uwanka ya kama da wuta to ka shafa wa naka ruwa" inda suka fara tsaurara matakan tsaro.

Kasar Somaliya ita ce gidan 'yan kungiyar ta al-Shabab da suka dauki nauyin kai wannan hari, kuma tuni mahukuntan kasar suka fara daukar matakan ko ta kwana.

A hannu guda kuma Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa dake birnin "The Hegue" na kasar Netherlands, da a yanzu haka take tuhumar mataimakin shugaban kasar Kenya mai ci wato Williams Ruto, da aikata laifukan yaki, ta ba shi hutun mako guda domin ya koma kasarsa ya taimaka wajen shawo kan wannan matsala.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani