1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenyatta ya halarci zaman kotun ICC

Lattefa Mustapha Ja'afarOctober 8, 2014

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya halarci zaman kotun kasa da kasa da ke hukunta masu aikata manyan laifuka wato ICC, domin ya kare kansa bisa tuhumar da kotun ke masa.

https://p.dw.com/p/1DSEe
Hoto: Reuters/Peter Dejong

Kotun ta ICC da ke da Helkwatarta a birnin The Heague na kasar Neatherlands na zargin Kenyatta da haddasa rikicin bayan zabe da ya gudana a kasar ta Kenya a shekara ta 2007 zuwa 2008, wanda kuma ya haddasa asarar rayuka masu yawan gaske. Steven Kay shine lauyan da ke kare Shugaba Uhuru Kenyatta, kuma a jawabin da ya yi a gaban kotun, ya bukaci ta yi watsi da karar da aka shigar gabanta saboda rashin wadatattun shaidu yana mai cewa....

1. O-Ton Steven

"Yana da 'yancin a yanke masa hukuncin rashin samunsa da laifi, kasancewar an gaza gabatar da gamsasshiyar shaida bisa wannan tuhuma da ake masa. Saboda haka wannan zargin da ake masa zargi ne mara tushe da ba hujja kwata-kwata."

Shugaban kasa mai ci na farko a gaban ICC

Shi dai Uhuru Kenyatta shine shugaban kasa da ke kan karagar mulki na farko da ya halarci zaman kotun ta ICC, duk da ya ke cewa kafin tafiyarsa zuwa birnin na The Heagua a kasar Neatherlands domin kare kansa daga tuhumar aikata laifukan yaki da ake masa, ya mika ragamar mulkin ga mataimakinsa William Ruto da shima ke fuskantar irin wannan tuhuma.

Germain Katanga ICC Den Haag Urteil 23.05.2014 Opfervertreter
Alkalai a kotun ICC da ke birnin The HeagueHoto: picture-alliance/dpa

A nasa bangaren daya daga cikin alkalan da ke sauraron tuhumar da ake yiwa Kenyatta Benjamin Gumpert ya zargi gwamnatin kasar ta Kenya ne da janyo tsaiko da kuma tafiyar hawainiya a wannan shari'ar inda ya ce...

"Wanda ake zargi a ganina shine yake janyo tsaiko a wannan shari'a da gan-gan. Babu bukatar wannan tafiyar hawainiya da shari'ar ke yi. Jinkirin ba shi da nasaba da rashin daukar abun da muhimmanci daga masu gabatar da kara, bashi da nasaba da wadanda ke sauraron shari'ar. Jinkirin na faruwa ne dangane da matakan da gwamnatin Kenya ke dauka a kan shari'ar wadda kuma ita ce ke da iko a kan wanda ake zargi."

Baiwa shaidu cin hanci da yi musu barazana

Shima lauyan da ke kare bangaren masu kara Fergal Gaynor ya zargi mahukuntan kasar ta Kenya ne da kokarin tursasa shaidu ta hanyar yi musu barazana da basu cin hanci da kuma bin duk wata hanya da suke ganin zasu iya bi domin hana ruwa gudu a shari'ar, yana mai cewa ba a yiwa iyalan wadanda aka kashe ko kuma aka yiwa fyade tare da azabtar dasu a lokacin rikicin bayan zaben adalci ba. Gaynor ya kara da cewa....

Afrika Bürger Zivilisten Gewalt Waffen Machete
Rikicin bayan zabe na 2007 zuwa 2008 a Kenya.Hoto: picture-alliance/AP Photo

"In har wanda ake zargi na son ya wanke kansa daga tuhumar da ake yi masa da ya yi iyakar iyawarsa wajen tabbatar da cewa ba a samu shaidu daga wayoyin salula da aka bukaba wanda kuma ke da alaka da shi a yayin rikicin bayan zaben. Wannan shine zai zamo hanya mafi sauki da zai wanke kansa daga zargi. Sai dai har yanzu yana iya yin hakan."

Kotun dai ta dage zamanta zuwa Alhamis dinnan wanda kuma daga nan ne za a yanke hukuncin gurfanar da shi gaban kuliya ko kuma yin watsi da karar baki daya. Shugaba Uhuru Kenyata wanda ya halarci zaman kotun da kwarin gwiwarsa kuma ba a matsayin shugaban kasa ba, bai ce uffan ba har aka kammala zaman sai dai bayan kammalawar ya yi jawabi ga magoya bayansa da suka yi masa rakiya zuwa kotun yana mai cewa, ya halarci zaman kotun kamar yadda suke bukata kuma har yanzu basu da wata kwakkwarar shaida da za ta tabbatar da cewa ya aikata laifin da ake zarginsa da shi.