1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kerry. Takunkuman Amirka za su ci gaba kan Iran

Mohammad Nasiru AwalJanuary 21, 2016

Sakataren harkokin wajen Amirka ya ce takunkumin kasarsa kan Iran suna nan daram don tinkarar take-taken karya dokokin kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/1Hhzp
Österreich Wien Atomverhandlungen USA Iran IAEA - Javad Zarif
Hoto: Reuters/L. Foeger

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce Amirka na kan bakanta na ci gaba da amfani da takunkumin kasar kan Iran, kuma za ta yi amfani da takunkuman wajen tinkarar duk wani take-taken da ta yi amanna sun karya doka. Kerry na mayar da martani ne ga korafin da Iran ta yi cewa Amirka ta dage kan kakaba wa Iran din takunkumi a lokacin da ya gana da Firaministan Iraki Haidar al-Abadi a yankin shakatawa na Davos da ke kasar Switzerland, inda ake gudanar da taron shekara shekara kan tattalin arzikin duniya.

Kerry ya ce:

"Mun nunar a fili cewa muna amfani da takunkumi a inda muka ga ya dace domin tinkarar wasu lamura da suka karya doka ko ke zama kalubale ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ko kuma barazana ga Amirka. Saboda haka muna tsaye daram kan batun takunkuman."