1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kinshasa: Bazaranar yunwa a yankin Kasai

Salissou Boukari
May 24, 2017

Yara kusan dubu 400 ke cikin hadarin kamuwa da cutar Tamowa a yankin Kasai da ke tsakiyar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango a cewar kungiyar UNICEF.

https://p.dw.com/p/2dWlv
Kongo Kananga Tshimbulu MONUSCO
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya na sintiri a yankin KasaiHoto: Reuters/A. Ross

Cikin wata sanarwa ce da UNICEF din ta fitar, ta ce ringingimun da ke gudana a yankin na Kasai, na shafar ayyukan kiwon lafiya sosai a watanni uku na baya-bayan nan, wanda hakan ke da hadarin saka wannan adadi na yara dubu 400 cikin mawuyacin hali na yunwa. Asussun kula da kananan yaran na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yana bukatar kudade da yawansu ya kai dala miliyan 40,2 domin fuskantar wannan matsala cikin gaggawa.

Tun dai daga watan Satumba da ya gabata, yankin na Jihar Kasai ke fama da matsalar rikicin 'yan tawaye na kungiyar Kamwina Nsapu, kungiyar da ta dauki sunan basaraken galgajiyar yankin da aka kashe a watan Augusta na 2016 yayin wani samamae da sojojin gwamnatin kasar suka kai.