1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira ga Isra'ila kan kariyar yaran Falasdinu

Salissou BoukariJune 18, 2015

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya nemi da Isra'ila ta dauki matakin da ya dace don kariyar yaran Falasdinu.

https://p.dw.com/p/1FjS9
Ban Ki-moon
Ban Ki-moonHoto: picture-alliance/dpa/I. Kovalenko

Ban ki Mooya yi wadannan kalammai ne yayin da yake buda taron mahawara na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bisa makomar yara kanana a lokacin yaki. Ya kara da cewa, yana mai cike da damuwa dangane da wahalhalun da yaran na Falasdinu suke fuskanta sakamakon matakin sojan da Isra'ila ta dauka a yankin na Zirin Gaza, sannan ya yi kira ga Isra'ila da ta sake duba tsarinta na yaki don kauce wa kashe-kashen yara kanana ko raunatar da su. Akalla dai yara fiye da 500 ne na Falasdinawa suka rasu yayin wannan rikici.