1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira ga kawo karshen rikicin kasar Libiya

December 17, 2014

Shugabannin Afirka da suka halarci taro kan zaman lafiya a Dakar, sun yi kira ga kasashen yamma da su daidaita matsalar rikicin Libiya da ke kawo cikas ga zaman lafiyar Sahel.

https://p.dw.com/p/1E5zh
Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Fiye da shekaru uku bayan da kungiyar tsaro ta NATO ta kaddamar da matakin sojan da ya haddasa kifar da Gwamnatin marigayi Mouammar Kadhafi, har kawo yanzu wannan kasa na cikin tsaka mai yuwa sakamakon rashin samun wata tsayayyar gwamnati da zata hada kan 'yan kasar.

Wannan matsala ta baiwa dubban 'yan ta'adda damar kafa sansanoninsu a wannan kasa, inda a halin yanzu su ke ci gaba da kasancewa barazana ga kasashe kamar su Mali, Nijar da kuma Chadi. Da yake maga kan wannan batu, Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita cewa yayi muddin dai ba'a kawo karshen matsalar kasar ta Libiya ba, to baza'a samu kwanciyar hankali ba a yankin Sahel.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu