1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira ga sabuwar gwamnati ta ceto 'yan matan Chibok

Al-Amin Suleiman MohammedApril 16, 2015

Iyaye da 'yan uwan 'yan matan sakandaren garin Chibok sun nemi sabon shugaban Najeriya yayi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an dawo musu da 'ya'yansu.

https://p.dw.com/p/1F9P2
Symbolbild Entführungen von Frauen und Mädchen in Nigeria
Hoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

Shekara guda kenan da 'yan kungiyar Boko ta sace 'yan mata sama da 200 a wata makarantar sakandare da ke garin Chibok a jihar Borno kuma har yanzu babu wani sahihin labari a kan inda suke ko a raye ko kuma ta Allah ta kasance da su.

Sace wadannan 'yan mata dai ya ja hankulan kasashen duniya inda aka zargi gwamnatin tarayyar Najeriya da sakaci wajen kasa kwato 'yan matan ko ma sanin hakikanin halin da suke ciki.

Kungiyar Jama'atu Ahlul Sunna da aka fi sani da Boko Haram wacce ta tabbatar da sace 'yan matan ta ce ta sayar da wasu, wasu kuma suna a hannunta.

Iyaye da 'yan uwa da abokan arziki dai musamman wadanda suke kauyukan Chibok na ci gaba da bayyana damuwa da kukansu tare da fatan cikin kankanin lokaci za a sanar da su halin da 'yan matan ke ciki ko ma akwato su don dawo da su gida.

Rashin taimako daga gwamnati

Ko yaya rayuwa iyaye da 'yan uwan wadannan 'yan mata ta kasance a cikin wannan shekara? Bulama Jona na garin Chibok daya daga cikin iyayen 'yan matan ya ce su fa har yanzu suna cikin damuwa domin ba a samu wanda ya taimakesu ba.

Vater des Chibok-Mädchens
Ali Mai Yanga mahaifin biyu daga cikin 'yan matan Chibok da ke hannun Boko HaramHoto: DW/Abdul-raheem Hassan

To ganin an samu sabuwar gwamnati da suke kyautatawa zato ya sa suka nemi shugaba mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari da yayi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an dawo musu da 'ya'yansu inji Malam Goni Chibok.

Tuni dai shugaba mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ceto 'yan mata matukar suna raye.

Ko yaya al'ummar garin Chibok suka ji da wannan matsayi na Janar Buhari, Mustapha Gana a Chibok ya ce suna yi wa shugaban fatan alheri kan alkawarin da yayi na ceto 'yan matan.

Shekara cikin zaman bakin ciki

Masu gwagwarmayar ganin an ceto wadannan 'yan mata kamar Dr Elisa Danladi ta kungiyar bunkasar matan nahiyar Afirka na ganin sun shekara cikin bakin ciki dangane da sace 'yan mata.

Boko Haram will Mädchen freilassen
'Yan #BringBackOurGirls suna magana da Rebecca Isaac (hagu) 'yar Chibok da ta tsere daga hannun Boko HaramHoto: AFP/Getty Images/P. Utomi Ekpei

Sai dai al'ummar wannan yankin sun bai wa manema labarai shawara cewa su rika tuntubarsu a kan abubuwa da suka shafe su maimakon mai da hankali kan masu gwagwarmayar ceto 'yan matan wato BringBackOurGirls.

Dukkanin iyayen 'yan matan dai sun bayyana cewa babu wani taimako da gwamnati ta musu wanda ya isa hannayen

su kuma sun fi bukatar a ceto musu 'ya'yansu sama da duk wani taimako da za a basu a wannan lokaci.