1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiran daina rufa-rufa a cin zarafin Baga

Zainab MohammedJuly 1, 2013

Kungiyoyin kare hakkin jama'a a Najeriya sun yi hamdala game da zargin sojoji da wuce gona da iri da hukumar kare hakin dan Adama ta yi,inda suka bukaci a dauki matakai.

https://p.dw.com/p/18zbS
A watan Afirilun 2013 aka yi kashe-kashe a Baga na NajeriyaHoto: picture alliance/AP Photo

A karon farko hukumar kare hakin dan Adam ta Najeriya ta fitar da rahoto da ta zargi jami'an tsaro da cin zarafin al'uma a farmakin da suka kai a garin Baga a cikin watan Afrilun da ya gabata, lamarin da ya haifar da mai da martani daga kungiyoyin kare hakin jama'a da ke kasar. Rahoton ya nuna sauyi daga yadda aka santa a shekarun baya, inda a wannan karon ta fito karara a fili ta bayyana cewa an gana wa fararen hula azaba tare da kullesu ba bisa ka'ida ba tare da cin zarafin mata a ikirarin da jami'an tsaro suke yi na yaki da masu kai hare-hare.

Abinda ya fi daukan hankalin jama'a shi ne yadda hukumar da gwamnatin Najeriyar ce ta kafata ta samun kwaurin guiwar fitowa a fili ta bayyana cewa an take hakin jama'a, bayan kuwa gwamnatin Najeriyar kiri-kiri ta musanta cewa an aikata hakan. Wannan ya sanya tambayar Kola Banwo na gamayyara kungiyoyin kare hakin jama'a da ke jigo a wannan hukuma da ta yi binciken , ko me wannan ke nunawa a yanzu?

"Wannan ya na da ban sha'awa domin muna jin gaskiya daga hukumar da gwanati ce da kanta ta kafata domin da ma tun da abin ya faru an ce an take hakin jama'a, amma aka ce ba'a yi ba. Kungiyoyin da ke kasashen waje ko hukumar da gwamnati da kanta ta kafa ta je ta gudanar da bincike kafin ta zo ta tabbatar da an take hakin jama'a. To muna fata za su dauki mataki su je gaba su matsa wa gwamnati. Muna fatan za'a samu ci gaba a gudanar da hukunci yadda ya kamata."

Bisa la'akari da yadda hukumar ta gudanar da bincikenta kafin kaiwa ga fitar da wannan rahoto inda ta yi tambayoyi ga mutanen da abin ya shafa wadanda ke cikin mawuyacin hali, ya sanya Malam Umar Faruq na kungiyar FCJJ bayyana cewa akwai bukatar daukan matakai na sadidan.

"A samu sahihin bayanai na dalilan da suka kawo wadannan rigingimu wannan shi ne hanyar da za'a duba a ga cewa ba'a samu wadanan rigingimu ba. A tabbatar da cewa wannan abin bai sake faruwa ba, ta yadda za'a zakulosu a tabbatar da cewa irin wadannan abubuwa ba su sake faruwa ba"

Gaskiya ta kamar hanyar yin halinta a Baga

Sanin kowa ne cewa a lokutan baya hukumomi irin na kare hakin jama'a ta Human Rights Watch da ma Amnesty International sun bayyanar da shaidun da suka tabbatar da zargin cewa jami'an tsaron Najeriya sun take hakin jama'a a mumunan harin da aka kai a garin na Baga amma kuma gwamnati ta musanta tare da ma yin watsi da rahoton. Amma a yanzu da hukumar da ta kafa da bi sahun na kasa da kasa ko wane sakamako wannan ka iya haifawarwa a kokarin da ake na kamanta adalaci a wannan lamari? Awwal Musa Rafsanjani shi ne shugaban kungiyar kare hakin jama'a ta CiCILAC da ke fafutuka a kan wannan batu.

"Sakamakon da wanan zai iya haifarwa shi ne dole ne gwamnati ta tashi ta daina karyace-karyace. Dole gwamnati ta tashi ta tabbatar ta kare hakin jama'a a Najeriya, saboda gwamnati ta sa hannu a kungiyoyi na kasa da kasa irin su Majalisar Dinkin Duniya, wanda ta yi alkawarin za ta kare hakin jama'a na 'yan kasarta. Don haka za mu tabbatar da cewa mun raba wannan rahoto a kasashen duniya don a sani, saboda yadda za'a daina wannan boye-boyen da ake yi ana cin zalin jama'a a ringa ganin Kaman ba komai a cikin abin"

Sabanin alkaluma game kashe-kashen Baga

Hukumomin tsaron Najeriya dai sun kasance masu musanta duk wani zargi na take hakkin jama'a kamar yadda Birgediya Janar Chris Kolade ya taba bayyanawa a kan wannan lamari. A yayin da har yanzu mahukunta ke jayeyaya a kan yawan mutanen da aka kasha a harin na baga da kungiyoyi suka bayyana sun kai 200 gwamnati na cewa 34.

Rahotannin cikin sauti na kasa

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe