1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiran firaministan Mali ga ECOWAS

December 27, 2012

Firaministan Mali Diango Cissoko ya nemi kasashen Afirka afkawa masu kaifin kishin addini cikin hanzari domin kubutar da yankin arewaci daga halin da ya ke ciki.

https://p.dw.com/p/179jp
Hoto: AFP/Getty Images

Firaministan Mali Diango Cissoko ya yi fatan ganin kasashen Afirka sun hanzarta turawa da sojoji yankin arewacin kasar domin kubutar da shi daga hannun masu kaifin kishin addinin musulunci. A lokacin da ya ke bayani ga manaima labarai bayan ganawarsa da shugaban Côte d Ivoire kana shugaban ECOWAS ko CEDEAO Alassane Ouattara, firaministan ya ce kasarsa za ta hanzarta daukan matakan da suka wajaba domin sauwaka wa dakarun kasa da kasa yin aiki cikin nitsuwa.

Diango Cissoko na rangadin wasu kasashe na yammacin Afirka da suka hada da Burkina Faso da Benin da Senegal domin neman shugabanninsu su taimaka wa Mali warware rikicin arewacin kasar da ke addabarta. Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tura sojoji arewacin Mali ba tare da tsayar da lokaci ba. Hakazalika ta jadadda bukatar tattaunawa da 'yan bindigan da ke nesanta kansu daga aiyukan ta'addanci domin mayar da Mali tsintsiya madaurinki daya.

Tun dai a watan yuni ne yankin arewacin Mali ya fada hannun kungiyoyin da ke da kaifin kishin addinin musulunci ciki kuwa har da reshen alQaida a yankin Magrib wato AQMI.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi