Kiran gurfanar da Assad gaban kotu
November 10, 2012Luis Moreno Ocampo ya ambata hakan ne yayin wata hira da kafar watsa labaran Canada ta CBC ta yi da shi a jiya Juma'a inda ya ce hakan ya zama wajibi saboda irin ɗumbin laifukan yaƙin da ya ce dakarun da ke biyayya ga shugaba Assad ke tafkawa a cikin ƙasar a yaƙin da su ke yi da masu rajin kawo sauyi.
Tsohon mai gabatar da ƙarar ta ICC ya ce ɗaukar wannan mataki na kame Assad ɗin bisa la'akari da yadda ake kisan fararen hula a ƙasar ita ce hanya ɗaya tilo da za a bi wajen kawar da ricikin da ƙasar fama da shi tun cikin watan Maris ɗin shekarar da ta gabata.
To sai dai yayin da Mr. Ocampo ke waɗannan kalamai, a hannu guda kuma ya ce baya goyon bayan yin amfani da tsinin bindiga wajen kawar da Assad daga karagar mulki domin kuwa hakan ba hanya ba ce mai ɓullewa.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Halima Balaraba Abbas