1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiran zanga-zanga duk da fargabar yaki a Burundi

Yusuf BalaMay 18, 2015

Wasu ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai na bin rukunin jama'a suna bayyana cewar za su ƙarar da su, abin da ya ƙara sawa mutane ke gudu.

https://p.dw.com/p/1FRAV
Burundi Militärputsch gescheitert
Masu zanga-zanga a BurundiHoto: Reuters/G. Tomasevic

Shugaban ƙasar Burundi Pierre Nkurunziza a ranar Lahadi ya bayyana karon farko tun bayan yunƙurin yi masa juyin mulki da ya gaza yin nasara, inda ya yi gargaɗin cewar akwai babbar barazana da ake fiskanta daga ɓangaren mayaƙan Ƙungiyar Al-Shabab sai dai a cewarsa komai na tafiya dai dai a Ƙasar.

Shugaban da ya bayyana a birnin Bujumbura, inda cikin murmushi ya riƙa gaisawa da 'yan jarida, ya dai yi wasu bayanai ba tare da taɓo batun yunƙurin yi masa juyin mulki ba, koma batun shirinsa na tazarce a karo na uku.

Tuni dai ƙungiyoyin da ke adawa da shugaba Nkurunziza suka bukaci jama'a su fito a ranar Litinin ɗin nan dan ci gaba da zanga-zanga.

Al'ummar wannan ƙasa dai tuni suke ci gaba da ficewa daga kasar saboda fargabar abin da ka iya zuwa ya dawo, inda ya zuwa yanzu sama da mutane 100,000 ciki yara ƙanana da mata na neman mafaka a kasashe da ke makwabtaka da ƙasar irinsu Tanzaniya da Jamhuriyar Demokradiyar Kwango.

Wani malami da ba ya so a bayyana sunansa ya yi karin haske kan halin da suke ciki:

"Dalilin mu na zuwa nan shi ne a gida bamu da kwanciyar hankali saboda muna jin tsoron matasa masu dauke da bindiga na kungiyar Imbonerakure saboda suna zagayawa suna tsoratar da mutane cewa za su karar damu".