1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kisan wani dan Burtaniya a Aljeriya

January 17, 2013

Burtaniya ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin 'yayanta da ake garkuwa da su a Aljeriya. Wata kungiya da ke da alaka da alqa'ida ce ke ta kame mutane 41a Saharan kasar.

https://p.dw.com/p/17LS7
Hoto: picture-alliance/dpa

Ministan harkokin wajen Burtaniya William Hague ya tabbatar da mutuwar wani dan kasarsa da ke cikin rukunin turawa da masu kaifin kishin addini ke garkuwa da su a Aljeriya. Da ma dai tun a jiya takwaran aikinsa na Aljeriya ya baiyana cewa biyu daga cikin bakin da ake garkuwa da su sun rigamu gidan gasdkiya.

Mutane 41 ne dai wata kungiya da ke da alaka da Alqa'ida ta yi garkuwa da su a wata cibiyar hako iskar gaz da cikin yankin saharan Aljeriya, daga cikinsu kuwa har da amurkawa bakwai da faransawa biyu da 'Yan Birtaniya biyu da kuma mutane biyu da suka fito daga Japan. Masu tsaurin kishin Islaman dai sun yi barazanar tarwatsa cibiyar ta iskar gaz idan hukumomin Aljeriya suka kuskura kai musu hari.

Wannan matakin dai na zama martanin ne ga matakin da hukumomin Alger suka dauka na bai wa Faransa izinin amfani da sarrarrin samaniyarta domin yakar masu kaifin kishin addinin Mali da suka dara kasar gida biyu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita:Umaru Aliyu