1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen yammacin Afirka na neman yin kudin bai daya

June 28, 2019

Shugabannin kasashen yankin yammacin Afirka na shirin yanke hukuncin karshe game da yiwuwar gammaya ta kudade a tsakanin kasashen yankin 15,Sai dai da alama akwai rashin fahimtar juna tsakanin shugabannin.

https://p.dw.com/p/3LItX
Westafrikas Staatschefs bei ECOWAS Summit
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

A taron da zai gudana a ranar (29-06-19) na shugabannin kasashe na yankin yammacin Afirka a Abuja tarrayar Najeriya za a san shawarar karshe da kasashen suka yanki. Sai dai kafin taron tun farko Najeriya ta soma nuna yin dari-dari da shirin kudin bai dayan. Duk da cewar dai tun daga shekara ta 2000 ne dai kasashen suka fara tunani na kirkiro kudi na bai daya a tsakanin al’ummar yankin yammacin Afirka kusan miliyan 300, har ya zuwa yanzu dai siyasar gado da kila tsoron-tsoro dai na ci gaba da jawo kila wakala game da kudin na bai daya a tsakanin kasashen .