1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko Mali ta doshi hanyar zama wata Afghanistan a Afirka?

March 1, 2013

Ana yawaita kwatanta yakin da ake yi da masu kishin addini a Mali da wanda ake yi da 'yan Taliban a Afghanistan sai dai wannan ba zai taimaka wajen warware rikicin ba.

https://p.dw.com/p/17oeY
A soldier from the Tuareg rebel group MNLA holds an AK-47 in the northeastern town of Kidal February 4, 2013. Pro-autonomy Tuareg MNLA fighters, whose revolt last year defeated Mali's army and seized the north before being hijacked by Islamist radicals, have said they are controlling Kidal and other northeast towns abandoned by the fleeing Islamist rebels. Picture taken February 4, 2013. REUTERS/Cheick Diouara (MALI - Tags: POLITICS CIVIL UNREST CONFLICT) // eingestellt von se
Hoto: Reuters

A babban labarinta game da rikicin Mali jaridar Süddeutsche Zeitung, ta fara ne da aza tambar shin wata Afghanistan a Afirka. Sannan sai ta ci-gaba kamar haka.

"Ana yawaita kwatanta yakin da ake yi da masu kaifin kishin addini a Mali da wanda ake yi da 'yan taliban a Afghanistan sai dai wannan ba zai taimaka wajen kawo karshen wannan rikici ba. Ana gwabza yaki gadan gadan a Mali to amma da alama yanzu ne matakan sojin a kan masu jihadin ya shiga wani mataki mai wahala, domin a daidai lokacin da ake murnar fatattakarsu daga wuraren da suka kama, sai ga shi sun koma wani yaki irin na sari-ka-noke, inda a cikin mako daya bangarorin dake fada da juna suka yi asarar sojoji ko dai sakamakon musayar wuta ko kuma harin kunar bakin wake a arewacin Mali. Hakika akwai wuraren da za a iya kwatanta wannan rikicin da na Afghanistan, amma abu mafi a'ala shi ne a shiga tattaunawa da 'yan tawayen Abzinawa, matakin da Faransa wadda ta yi ruwa ta yi tsaki a cikin rikicin, ke matsa lamba da a yi."

Kokarin samar da zaman lafiya a Kongo

Shin za a samu zaman lafiya a Kongo kuwa? Wannan tambaya ce da jaridar Die Zeit ta yi tana mai nuni da yarjejeniyar zaman lafiyar da kasashe 11 da kuma kungiyoyin kasa da kasa hudu suka sanya wa hannu.

"Wannan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya a Kongo na matsayin wani babban lamari a diplomasiyance, ta hana yin katsalanda a rikicin kasashe makota, da taimaka wa kungiyoyin 'yan tawaye, sannan tana da nufin kawo karshen wani yaki da aka shafe shekaru da yawa ana yi tsakanin bangarori daban daban, wanda kuma ya janyo asarar rayukan mutane kusan miliyan biyar. A waiwaye adon tafiya, an kulla yarjeniyoyin zaman lafiya da yawa ga kasar ta Kongo amma dukka sun wargaje a saboda haka babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, wanda ya halarci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar Lahadi da ta gabata, ya ce an bude wani babin wani shiri na dogon lokaci. Shi dai Ban ba ya son sunansa ya shiga cikin littafan tarihi cewa a lokacinsa ne wani aikin tawagar Majalisar mafi tsada kuma mafi girma ya gaza. Sai dai babbar ayar tambaya a nan ita ce ko sassan da abin ya shafa za su girmama wannan shirin zaman lafiyar?"

U.N. Secretary General Ban Ki-moon (C) arrives for the signing ceremony of the Peace, Security and Cooperation Framework for the Democratic Republic of Congo and the Great Lakes, at the African Union headquarters in Ethiopia's capital Addis Ababa Feburary 24, 2013. A U.N .-mediated peace deal aimed at ending two decades of conflict in the east of the Democratic Republic of Congo was signed on Sunday by leaders of Africa's Great Lakes region in the Ethiopian capital Addis Ababa. REUTERS/Tiksa Negeri (ETHIOPIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Mr Ban na daga cikin wadanda suka rattaba hannu a yarjejeniyar zama lafiyar KongoHoto: Reuters

Fargabar tashin hankali a zaben Kenya

Ita kuwa jaridar die Tageszeitung labari ta buga game da zaben kasar Kenya da za a gudanar a ranar Litinin. Ta ce kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya bayan nan ta nuna ana kankankan tsakanin Raila Odinga na kabilar Luo da Uhuru Kenyatta na kabilar Kikuyu. Har yanzu dai ana zaman yi wa juna kallon hadarin kaji tsakanin kabilun na Luo da Kikuyu, abin da ke karfafa barazanar yin fito na fito tsakanin wadannan manyan kabilun guda biyu. Don kaucewa wani tashin hankalin shigen wanda aka fuskanta bayan zaben shekarar 2007, dukkan 'yan siyasar kasar na kira ga magoya bayansu da su guji ta da zaune tsaye.

A woman carries her baby as she walks past an Orange Democratic Movement (ODM) campaign poster in Kibera slum in capital Nairobi February 27, 2013. Kenya will hold its presidential and parliamentary elections on March 4. REUTERS/Siegfried Modola (KENYA - Tags: ELECTIONS POLITICS)
Ko Kenya za ta gudanar da zabe cikin lumana?Hoto: Reuters

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi