1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kofi Annan da wasu shugabannin Afrika suna Ivory Coast

Hauwa Abubakar AjejeJuly 5, 2006

Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Kofi Annan da wasu shugabannin Afrika sun gana da shugaban kasar Ivory Coast da shugabannin adawa yau inda suka yi kira ga gaggauta gudanar da zabe a kasar,domin karfafa zamana lafiyarta

https://p.dw.com/p/BtzO
Hoto: AP

:A ziyararsa karo na farko tun bayan yunkurin juyin mulki da bai yi nasara a kasar,wanda kuma ya raba kasar gida biyu,Annan ya isa ne tare da wasu manyan shugabanin Afrika wadanda suka taka rawa ga shirin zaman lafiya na kasar.

Shugaba OBJ na Najeriya,Thabo Mbeki na ATK,Denis Sassou Nguesso na Jamhuriyar Demokradiyar Kongo,wanda kuma shine shugaba mai ci yanzu na AU,sai kuma Tanja Mamadou na Nijar kuma shugaban ECOWAS.

Annan yayi niyar a gobe alhamis idan Allah ya kai mu,zai ci gaba da ganawa da shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast din,wanda suka fara tun ranar asabar wajen taron AU a Gambia.

Tawagar dai zata gana da firaminista Charles Konan Banny,wanda manyan shugananin duniya suka nada ya shugabanci shirin zaman lafiya da kuma shirya zabe a kasar a watan oktoba.

Gbagbo yace ziyara Kofi Annan zuwa kasar ivory Coast,zata taimaka wajen bude wani babi na sabuwar tattaunawa,a daya bangaren kuma zai duba ko Banny ya samu ci gaba mai maana wajen shirya zaben kasar.

Kofi Annan dai ya baiyana bukatar ganin an gudanar da wannan zabe cikin wannan shekara kamar yadda aka shirya tun farko,inda ya kara da cewa,ba zai yiwu a ci gaba da hali da ake ciki ba yanzu a kasar.

Annan zai tabbatar da cewa an kwance damarar dubun dubatar dakarun gwmantai dana sojin sa kai,tare shirya rajistar zabe a kasar.

Kasar ta Ivory Coast kuma zata karrama Annan saboda aiyukan da yayi cikin majalisar dinkin duniya cikin shekaru goma da suka shige.

Danganta dai tsakanin Ivory Coast da Majalisar Dinkin Duniya ta kara inganta ne,a 2004,a lokacinda shugaban kasar ya baiwa majalisar damar gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya mai girma,tare da taimakon kasar faransa.

Sai dai a watan janairu an samu sabani a lokacinda masu goyon bayan Gbagbo suka kai hari kan dakarun majalisar dinkin duniya,bayan yanke shawarar rushe majalisar dokokin kasar,yayinda waadin mulknisu yak are.

Saboda neman tsaron lafiyarsu,Majalisar ta janye jamianta daga kasar,har ma da hukumomin bada agaji,musamman ma wadanda suke kan iyakar kasar da Liberia.

Kodayake yanzu,abubuwa sun lafa,jamian Majalisar Dinkin Duniya sun koma bakin aikinsu,hakazalika wakilinta a kasar ta Ivory Coast Pierre Schori,yace,harkokin siyasa suna tafiya yadda ya kamata a kasar.

A watan daya gabata kuma komitin sulhu ya kara yawan dakarun majalisar daga 7,600 zuwa 9,100 wadanda suka hada da soji day an sanda.

Masu lura da almaura dai har yanzu suna nuna shakkun game da gudanar da zabe cikin yan watanni masu zuwa,ganin cewa har yanzu baa kamala kwance damarar yaki ba,haka kuma baa shirya rajistar masu jefa kuria ba.

Wani kuma mai lura da harkokin da ke kai su komo daga kasashen yamma,yace bai fidda zaton karawa Gbagbo da Banny waadi ba,ko da kuwa na yan watanni kalilian ne.