1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kofi Annan ya fara ganawa da mahukuntan Iran a birnin Teheran

September 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bukj

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya isa Iran inda yanzu haka yake tattaunawa da hukumomin kasar akan shirin nukiliya na gwamnatin Teheran da kuma halin da ake ciki a Lebanon. Ziyarar ta sa ta zo ne yayin da Amirka ke matsa lamba da a sanyawa Iran takunkumi bayan ta gaza cimma wa´adin kwamitin sulhu na ta dakatar da aikace aikacen inganta sinadarin uranium. Halin da ake ciki a Lebanon zai kasance kan gaba a ziyarar ta mista Annan a daidai lokacin da MDD ke kokarin kara yawan dakarun ta a kudancin kasar. Manufar rangadin sa na kwanaki 10 a yankin na GTT shi ne samun goyon bayan don aiwatar da kudurin kwamitin sulhu wanda ya kawo karshen rikici kwanaki 34 tsakanin Isra´ila da Hisbollah. A jiya juma´a Syria ta yi masa alkawarin girmama haramcin tura makamai ga ´yan Hisbollah.