1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin dakile yaduwar cutar Ebola

July 4, 2014

Kasashen Afirka ta Yamma sun dukufa wajen dakile yaduwar kwayoyin cutar Ebola da kawo yanzu suka hallaka rayukan daruruwan mutane a yankin.

https://p.dw.com/p/1CVoo
Ebola-Virus in Guinea
Hoto: Seyllou/AFP/Getty Images

Bari mu fara da jaridar Die Welt wadda ta yi tsokaci game da cutar Ebola da ke ci gaba yaduwa a wasu sassan kasashen Afirka ta Yamma.

Ta ce annobar Ebola mafi muni a wannan lokaci, ta janyo asarar daruruwa rayuka a Yammacin Afirka sannan tana ci gaba da yaduwa a saboda haka hukumar lafiya ta duniya WHO ta shirya wani taron gaggawa a birnin Accra na kasar Ghana da nufin magance kura-kuran da shugabannin suka tabka a baya tare kuma da gano hanyoyin dakile yaduwar cutar mai saurin kisa. Tun a cikin watan Afrilu a ziyarar da ya kai ofishin hukumar WHO a birnin Geneva shugaban kasar Guinea daya daga cikin kasashe Afirka ta Yamma da cutar ke wa ta'adi ya ce sun shawo kanta kuma yayi fatan ba za a sake samun barkewar annobar cutar ba. Jaridar ta Die Welt ta ce wannan babban kuskure da shugaban ya yi, ya janyo asarar rayukan mutane. Yau fiye da watanni biyu baya halin da ake ciki a Yammacin Afirka dangane da cutar na barazanar zama gagarabau, inda cutar ta fi shafar kasar ta Guinea.

Matakan gaggawa don dakile Ebola

Ebola-Virus Guinea
Hoto: picture alliance/AP Photo

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta sharhi a kan cutar ta Ebola, tana mai cewa watanni shida ke nan kwayoyin cutar Ebola ke yaduwa a kasashen Guinea da Saliyo da kuma Laberiya kuma tana iya shiga wasu kasashe nan ba da jimawa ba. Jaridar ta rawaito daraktan hukumar WHO a Afirka Luis Sambo na cewa yanzu annobar ta fi karfin kasa guda daya. Saboda haka hukumarsa ta yi kira da a dauki matakan gaggawa, a saboda wannan dalili ne aka shirya babban taron ministocin kiwon lafiya na kasashe 11 na Afirka ta Yamma a ranakun 2 da 3 na watannan na Yuli a birnin Accra. Sambo ya nuna damuwa matuka game da yiwuwar yaduwar cutar zuwa wasu kasashen duniya.

Kuncin rayuwa ga 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu

A wannan makon jaridar Die Tageszeitung ta leka kasar Sudan ta Kudu ne inda ta labarto mawuyacin hali da 'yan kasar su kimaninn dubu 450 ke ciki a wani sansani da ta kwatanta da na kunci.

Südsudan Flüchtlingslager
Hoto: Reuters

Ta ce karancin ruwan sha, da neman itacen girki cikin yanayi mai hatsari da karancin abinci da barkewar cututtuka suna karuwa a sansanin da a cewar jaridar ya yi wa mutane kimanin dubu 450 kadan matuka. Ta ce tun a cikin watan Disamban bara 'yan gudun hijirar ke neman wuri da ke zama tudun mun tsira, bayan barkewar rikicin kasar tsakanin dakarun gwamnatin shugaba Salva Kiir da na 'yan tawaye karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar. Sojojin Majalisar Dinkin Duniya ke samar da tsaro ga sansanin, inda kungiyar likitoci masu ba da agaji ke kula da marasa lafiya kana kuma suna binne wadanda suka mutu ba kawai marasa lafiya ba a'a har ma da wadanda aka tilasta musu barin yankunansu na asali kuma suka gamu da ajalinsu a sansanin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar