1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Jamus da Isra'ila

Mouhammadou Awal BalarabeFebruary 16, 2016

Magabatan kasashen biyu na tattaunawa a Berlin inda shugabar gwamnati Merkel da Firaminista Netanyahu za su tattauna rikicin Syriya da yarjejeniyar nukiliyar Iran.

https://p.dw.com/p/1HwA1
Deutschland Israel Netanjahu bei Merkel
Hoto: Getty Images/AFP/O. Andersen

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da manyan ministocinsa na gudanar da taron majalisar ministocin na hadin gwiwa da takwarorinsu na Jamus a wannan Talatar a birnin Berlin.

Jirgin karkashin ruwa da Jamus ta samar wa Isra'ila, shi ne babban mizanin da ke gwada karfin dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu. A tashar jirgin ruwan Haifa a ranar 12 ga watan Janairu ne rundunar sojojin ruwan Isra'ila ta samu jirgin ruwan yaki da ke zama irinsa na biyar da aka kera a Jamus. Saboda haka ne shugaban wannan kasa Reuven Rivlin ya gode wa Jamus kan gudunmawar da take bai wa Isra'ila don kare kanta daga makiya.

"Wannan gudunmawa na jirgin ruwan yaki da aka yi wa lakabi da Rahav da sauran jiragen karkashin ruwan, ya nuna a zahiri da kuma a siyasance cewar tsaron Isra'ila na da muhimmanci a idanun Jamus ko da a lokacin banbancin manufofin siyasa."

Isra'ila za ta iya amfani da wadannan jiragen ruwan yakin don harba makamin kare dangi a wani mataki na barza tsakuwa don aya ta ji tsoro. Sai dai duk haka gwamnatin ta Isra'ila ta na ci gaba da nuna damuwa kan shirin nukiliyar kasar Iran, duk da yarjejeniyar da aka cimma da ita fadar mulki ta Teheran bisa taimakon tarayyar Jamus. Firaministan Benjamin Netanayu ya ce har yanzu da sauran rina a kaba.

Angela Merkel und Benjamin Netanjahu
Merkel da NetanyahuHoto: Lemmer/AFP/Getty Images

"Mun yi imanin cewar za a iya samun ci gaba fiye da wanda aka samu a tattaunawar birnin Lausane. Wannan mataki na da matikar muhimmanci ga makomar kasarmu da tsaron rayukanmu. Dul lokacin da na samu damar tattauna da Angela Merkel a kan wannan batu zan bayyana mata matsayi na kan kalubalen da ake fuskanta."

Gwamnatin Isra'ila ta kwana da sanin cewar ta na da danganta mai karfin gaske a fannin tsaro da Jamus, duk da sabanin da suka samu kafin Isa'ila da sayi jiragen na yaki. Herzl Makov shugaban cibiyar Menachen Begin da ke Birnin Kudus ya yaba wannan mataki.

"Babu tantama cewar marar jiragen karkashin ruwa abu ne mai kyau, musamman ma idan aka yi la'akari da rangwame da alakar siyasa da goyon bayan da muke samu daga Jamus. Amma akwai sarkakiya da ba a ransa ba. A fili yake cewar a fannin siyasa Merkel na goyon bayan Isra'ila duk da sabanin da take samu da Netanayahu a wasu fannonin. Sai dai a fannin shari'a da al'adu, Isra'ila ba ta samun karbuwa sosai."

Bundeskanzlerin Merkel trifft Israels Premierminister Netanjahu in Berlin
Zaman tattaunawa tsakanin magabatan kasashen biyu a BerlinHoto: Reuters/Bundesregierung/G. Bergmann

Fannin da aka fi samun rashin fahimta tsakanin Jamus da Isra'ila shi ne batun gine-ginen gidajen share wuri zauna da Yadawa ke yi a yamma da kogin Jordan. Ita kuwa Isra'ila ta na nuna bancin ransa dangane da matakain da kungiyar Gamayyar Turai ta dauka na maka tambarin da ake yi a kan kayayyakin da ake kerwa daga Isra'ila don nuna adawa da matakin da take dauka a kan Paesdinawa. A cewarta dai ko da Jamus ba ta yi nasarar shawo kawunan takwarorinta na Eu ba, amma bai kamata ta yi aiwatar da wannan mataki a kan Isra'ila ba. Ministan shari'a na Isra'ila Ayelet Shaked ya bayyana wa takwaransa na Jamaus Heiko Maas takaicinsa a kan wannan batu.

"Na bayyana wa takwararn aikina cewar maka tambari a kan kayayyakin da Isra'ila ke shigowa da su Turai, mataki ne da bai dace ba domin ya na dadada wa abokan Isra'ila rai tare da sa a kaurace ma kayayyakinta. Don haka na bukaci ministan shari'a da a hana maka wannan tambari musamman a nan Jamus."

Duk da sabanin ra'ayin da ake fuskanta tsakanin kasashen biyu dai, Jamus na ci gaba da zama wa Isra'ila abokiyar hulda da ta fi kowacce muhimmanci a nahiyar Turai.