1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin hade 'yan gudun hijirar Calais da iyalensu

Kamalu Sani ShawaiMarch 3, 2016

Firaminstan Birtaniya David Cameron da shugaban kasar Faransa Francios Halland na la'akari da yiwuwar hade 'yan gudun hijirar Calais da iyalensu.

https://p.dw.com/p/1I6wi
Frankreich Amiens Francois Hollande David Cameron (R)
Hoto: picture-alliance/dpa/Y. Valat

David Cameron da shugaban Francios Hollande na tattaunawa a kan batun yadda za su sake hade 'yan gudun hijirar Calais da iyalensu zuwa Birtaniya.

A yayin da David Cameron yake jawabi a birnin Paris a wannan Alhamis, ya yi nuni da cewar akwai bukatar yin aiki tare don sada 'yan gudun hijirar da iyalensu.

Da ya juya batun halin da 'Ya kasar Syriya suke ciki David Cameron yace.

Hakan zai iya samun sauyi ne kadi idan gwamnatin Syriya ta sauya dabi'arta gami da masu mara musu baya, wannan ne ma ya sanya gobe ni da shugaba Holand gami da Angela Markel zamu yi magana da shugaba Vladimir Putin na Rasha.