1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan:An koma tattaunawa neman sulhu

Mahmud Yaya Azare AH
June 12, 2019

A daidai lokacin da jagororin masu fafutuka na Sudan ke sanar da jingine boren gama garin da aka yi kwanaki biyu ana yi bangarori da ke rikicin sun amince da komawa kan teburin tattaunawa.

https://p.dw.com/p/3KEI5
Sudan Khartoum Vermittlung von äthiopischen Botschafter Mohamoud Dirir
Hoto: Ethiopian Embassy Khartoum

Banagrorin biyu sun lamunta da daukar matakan samar da amintar juna tsakaninsu don haka a yanzu majalisar soji ta lamunta da sakin dukkanin firsinonin siyasa da masu zanga-zangar da aka tsare. A yayin da su kuma masu fafutukar neman sauyi ke amincewa da jingine boren gama garin da suke yi, kakakin tawagar Kasar Habasha, Mahmud Darir wanda ya jagoranci tattaunwar ya ce ana kan hanyar samun masalha tsakanin bangarorin biyu. A hanu guda kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International  ta nuna damuwarta kan sake bullar mayakan Janjaweed a yankin Darfur, yadda suka harbe kimanin mutane goma da kone gidaje da shagunan mutanan da suka shiga boren gama gari a yankin.