1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin magance matsalar karancin abinci

Amin Suleiman MohammedOctober 16, 2013

16 ga watan Oktoban kowace shekara rana ce ta bukin ranar abinci da nufin yin nazari da bibiyar ayyukan gwamnatoci domin magance matsalar karancin abinci a duniya.

https://p.dw.com/p/1A0rm
Quelle: http://www.flickr.com/photos/69594481@N06/6460097741/in/photolist-aQRFZx-9Zrji9-5Phgbs-9QVzFb-4rPkbi-7g6iPS-ejvfoo Lizens:http://creativecommons.org/licenses/by-nd/2.0/deed.de +++CC/Twin and Twin Trading Images+++ Gandali MAC group, Kululu Chapter, Mchinji Groundnut field preparation 30.7.2007 geladen am 6.6.2013
Hoto: CC/Twin and Twin Trading Images

Hukumar kula da abinci da ayyukan gona ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware wannan rana domin fadakar da al'umma muhimmacin yaki da yunwa da karancin abinci mai gina jiki musamman ga yara tare da nuna goyon baya ga duk wani hobbasa na samar da abinci a duniya.

Bukin ranar ta bana dai na zuwa a dai-dai lokacin da ake fargabar samun matsalar karancin abinci saboda matsaloli da suka hada na gurbata muhalli da kuma sakacin gwamnatoci na kin maida hankali ga ayyukan gona.

Rashin kula da fannin noma

Ko wane matsaloli za a iya cewa harkokin noma da samar da abinci na fuskanta a nahiyar Afirka musamman tarayyar Najeriya? Malam Muhammad Ibrahim wani masani ne ke kan ayyukan gona a Najeriya.

"Irin abubuwan da suka faru irin na ambaliya sannan wasu wurare babu kwanciyar hankali, uwa uba su kuma hukumomi da al'amari ya shafa ba sa ba ma wannan sashe kulawar da ta dace."

Maisfeld in Kwadiya Dorf bei Dutse, Jigawa, Nigeria. 29.03.2013, Kwadiya, Jigawa / Nigeria Copyright: DW
Hoto: DW

Matsalar rashin tsaro dai ta tilasta manoma da dama a yanikin arewa maso gabashin Najeriya tserewa daga gonakinsu musamman ma jihar Borno da ke zama babban fagen fama a yaki da ake da ‘yan kungiyar Ahlul Sunna da aka fi sani da Boko Haram.

Yanzu haka kuma akwai al'ummomi a yankin jihar Yobe da suka koka da cewa jami'an tsaron sun haramta musu noma abubuwa masu tsayi kamar hatsi saboda magance fakewar mahara domin kai hare-harensu.

Wannan mataki da jami'an suka tabbatar da dauka da manufar cewa shawara suka bai wa al'umma ba wai tilasta su ba, na barazana ga shirin samar da abinci.

Wata matsalar kuma ita ce ta ambaliyar ruwa da ta lalata gonaki da dama da suka kasa nomawa a sassan Najeriya.

Wannan yasa na tambayi Alh Dahiru Buba Biri kwamishinan ayyukan gona na jihar Gombe ko wane mataki suke dauka don ganin wannan matsalar ta ambaliyar ruwa bata haifar da karancin abinci ba?

"A bana an samu ruwan sama isasshe da ya kamata a ce an samu amfani gona mai yawa amma a wasu wurare an samu ambaliya. Shi ya sa dole ne a bana a tallafa wa manoma da kayakin aiki na zamani kamar injunan noma da karin takin zamani da abubuwan da za su sa su yi noma rani."

food distribution of MSF in Angola
Hoto: picture-alliance/Ton Koene

Rashin amfanin wannan rana

Sai dai wasu kamar Sani Yaro Gombe na ganin yin bukin wannan ranar ba bashi da amfani in dai a tarayyar Najeriya ne domin sai an ci an koshi ake buki. Saboda haka ina mai jin yunwa zai wani buki?

Yanzu haka dai ana samun mutane masu yawa dake kwana da yunwa wadanda suka samu abincin ma sau daya ko biyu suke ci inda sai ka yi da gaske ka samu masu cin abinci sau uku a wasu sassan.

Amma akwai fata daga hukumar kula da noma da samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya wanda kan cewa za a samu raguwar yunwa a wasu sassa na duniya saboda damuna mai albarka da aka samu da kuma rubanya kokari da wasu hukumomin suka yi wajen samar da abincin.