1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin mawakin Opera Serge Kakudji a Kwango

Lateefa Mustapha JaafarDecember 9, 2015

A yunkurin cike babban gibin da ke tsakanin nahiyoyi Afirka da Turai, Serge Kakudji da 'yan kungiyarsa ta mawakan opera na amfani da salon kida na kasar Kwango da kuma nahiyar Turai wuri guda.

https://p.dw.com/p/1HJsN
Serge Kakudji
Hoto: DW/S. Oneko

An dai gano baiwar da Kakudji ke da ita tun yana dan shekaru bakwai da haihuwa yayin da yake waka a Coci ga yara a Lubumbashi na kasar ta Kwango. Daga bisani wannan baiwa ta kai shi Turai tun yana da shekaru 17. Tun daga wannan lokaci dai ba kasafai Serge Kakudji ke samun damar yin waka a kasarsa ta asali ba. Sai dai a wannan karon ya samu dama. Ya kuma bayyana farin cikinsa kamar haka:

"Abokaina da yawa za su zo saboda Kwongo kasata ce. Wasu kuma za su zo daga nesa. Ina farin ciki. Wasu ma sun ce min basa son su ganni kafin na fara wakar, sun fi so kawai su ganni a dandali."

Kongo Serge Kakudji Countertenor
Hoto: DW/S. Oneko

Kakudji da makadansa na "Coup Fatal" da suka hada da 'yan kasar Beljiyam biyu da kuma wani matashi dan kasar Kwango, sun kware a fagen gwama kayan kida na Kwangon da kuma salon kidan kasashen yamma na Baroque Opera. Yin wannan kida a Kinshasa wata hanya ce da Kakudji zai iya amfani da ita wajen cike gibin da ke tsakanin rayuwarsa ta Turai da kuma ta kasarsa ta gado wato Kwango. A matsayinsa na matashi ya rubuta waka ta opera da yarensa na Siwahili.

"Mutane da dama a nan na tambayar mu domin a Kwango ba a san wannan salon wakar ba. Muna jin dadinta saboda tana sosa zuciya, amma kuma sukan tambayeni me ne ne ra'ayin Turawa a kan hakan? Masu kallo na yi min wannan tambaya sau tari."

Duk da cewa Kakudji kullum yana zagaya duniya, amma kuma mawakin ya amince cewa babu inda yafi gida dadi inda yake cewa:

 

"Abinda nake kewa sosai shi ne rashin cudanya da mutane. Abin da mutum ke samu da zarar ya iso gida. A Turai babu irin wannan ma'amala, sai dai akwai a wasu wuraren, misali, idan muna wasa a kungiyarmu ta "Coup fatal" ina samun wannan ma'amala."

Kakudji da makadansa na yin rawa da juyi da kidan Rhumba da suka gada a Kwango da kuma kidan zamani na Bach da Handel. A bayyane take Kakudji mutum ne mai ruwa biyu, kuma yana jin dadin hakan.

"Ba zan iya cewa zan rayu a Turai ko kuma a Kwango ba. Ina rayuwa ne a sassan duniya biyu saboda akwai sako da nake isarwa ga kowanne bangare a karkashin al'adar da nake yadawa."

A shekara mai zuwa Kakudji zai gudanar da wakokinsa a Turai da Amirka. Ta hanyar fasahar da yake da ita, matashin mawakin zai cike kibin da ke tsakanin nahiyoyin biyu.