1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin NATO na warware rikicn Krimeya na Yukren

Mohammad AwalMarch 3, 2014

Kungiyar tsaro ta NATO ta bukaci a tura da masu sa ido na kasa da kasa zuwa Yukren domin warware takaddamar da ta ke fuskanta da Rasha cikin ruwan sanyi. Hakazalika ta yi kira ga Rasha da ta janye sojojinta a Krimeya.

https://p.dw.com/p/1BIgY
Anders Fogh Rasmussen NATO Russland Ukraine Krise Pressekonferenz
Hoto: Reuters

Sa'o'i takwas jakadun kasashe 28 da ke da kujera a kungiyar tsaro ta NATO suka shafe suna tattaunawa a kan matakin soje da Rasha ta dauka a tsibirin Krimeya na Yukren. Gaba dayansu dai sun yi magana da murya daya, inda suka yi tur da kutsen da Rasha ta yi a 'yantacciyar kasa, tare da kiranta da ta tattara nata ya nata ta fice daga Yukren. Babban abin da ya fito fili dai shi ne cewa NATO ko OTAN ta na fifita hanyar dipolomasiya wajen warware rikicin da ya kunno kai tsakanin Rasha da makobciyar kasa Yukren. Hasali ma dai ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta tura da wakilanta domin su sa ido a kan abubuwan da ka je ya zo.

NATO ba ta gayyaci Rasha a taronta ba

Babban bako a taron ya kasance wakilin Yukren, kasar da kungiyar ta NATO ta kulla kawance da ita. Sai dai kuma a daya hannun kungiyar ba ta gayyaci wakilin Rasha ba duk kuma da kasancewar kasar da ta haddasa wannan takaddamar. Saboda haka ne Harald Kujat, tsohon shugaban kwamitin tsaro a NATO ya ce babban kuskure ne.

Masanin tsaro Harald Kujat ya yi fashin baki game da rikicin Krimeya
Hoto: privat

"Zan so a ce an gudanar da taron hadin guywa tsakanin NATO da Rasha musamman ma karkashin ministocin harkokin wajensu. Wannan mataki ne zai iya yin tasiri sosai a Rasha. Da ma dai NATO ta hada kai da Rasha karkashin wani kawance da nufin kare muradun tsaro na NATO da ma dai na Rasha idan bukatar hakan ta taso."

Me NATO za ta iya yi a rikicin Yukren?

Sai dai kuma da kamar wuya NATO ta ba da taimako kai tsaye ga Yukren domin ta yakar Rasha saboda kasar ba ta da kujera a wannan kungiya. Matakin da mambobin kungiyar za su dauka ba zai fi tattaunawa kai tsaye da hukumomin Rasha domin warware rikicin cikin ruwan sanyi ba. Dalili kuwa shi ne Rasha ce kasa ta biyu a duniya baya ga Amirka da ke da karfin makamin nukiliya. Saboda haka ne kasashen duniya ke kaffa-kaffa da ita game da duk al'amuran da suka shafi fito na fito da makamai. Saboda haka ne ma Klaus Mommsen kwararren a al'amuran tsaro ke ganin cewa, ba abin da ya fiye wa NATO a rikicin Yukren illa ta zama 'yar Kallo.

"NATO za ta mayar da hankali ne kan hanyoyin da suka shafi siyasa. NATO ba ta kasance kungiya ta kare kasashe mambobinta ba kawai, a'a. Amma dai manufofinta sun sauya bayan rushewar daular Soviet, inda ta fara cundaya da Rasha karkashin hukumar hadin guywa ta NATO da Rasha ga misali."

Ita dai kasar ta Rasha ta saba yin kunnen uwar shegu ga gargadin da kasashe mambobin NATO suka saba yi mata a lokacin rikice-rikice na kasa da kasa. A shekara ta 2008 dai hukumomin Moscow sun yi gaban kansu a rikicin Georgia inda suka kutsa wannan kasa, tare da taimaka wa yankunan Osetiya ta Kudu da kuma Abkhaziya samun damar ballewa.

Har yanzu dai tsugone ba ta kare ba a kasar Yukren
Hoto: Reuters

Rasha za ta zama saniyar ware

Abin da ya fito fili dai shi ne kasar Rasha za ta iya zama saniyar ware, saboda kasashen nan bakwai da ke da karfin masana'antu a duniya na shirin daukan matakin kin halartan taron G8 da aka shirya gudanarwa a birnin Sotchi na Rasha. Sai dai ayar tambaya da kwararru ke dasawa ita ce, wannan matakin zai sa Rasha ta karkato daga inda ta dosa, ko kuma mataki ne na ran sarki ya dade? Kallo dai ya koma sama.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar