1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shirin daukar matasa aiki

Uwais Abubakar Idris LMJ
January 5, 2021

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da fara daukar ma'aikata dubu 774, a daukacin kananan hukumomin kasar, a kokarin rage rashin aiki da talauci musamman a tsakanin matasa.

https://p.dw.com/p/3nXi7
Nigeria Präsident Mohammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Wannan mataki dai ya  fuskanci takaddama tsakanin bangaren gwamnati da majalisar dokokin kasar. Daukar matasan dubu 774 a daukacin Tarayyar Najeriyar da gwamnatin kasar ta tsara dai, shi ne domin rage daruruwan matasan Najeriyar da suka kammala karatu ba tare da samun aikin yi ba.

Karin Bayani: Sabon adadin marasa aikin yi a Najeriya

An tsara  daukar masu sana'o'i iri dabam–dabam ne da za su yi amfani da abubuwan da ake samu a cikin kasar, domin bunkasa tattlin arziki da rage radadin talauci da samar da aikin yi. Sai da aka kai ruwana dai a tsakanin bangaren zartaswa da na majalisa, har ma da fadi in fada tsakanin ministan kasa a ma'aikatar kwadago ta Najeriyar Festus Keyamo da 'yan majalisar.

Neujahr in Nigeria
Baya ga rashin aikin yi, Najeriyar na fama da tarin matsaloli

Duk da dokin da ake na wannan shirin dai akwai tsoro na dorewarsa, sanin cewa watanni uku za a yi ana bai wa matasan albashin Naira dubu 20 daga nan kowa ya kama gabansa. Sai dai ministan kasa a ma'aikatar kwadago ta Najeriyar Festus Keyamo da ya kadammar da shirin, ya bayar da tabbacin cewa: "Muna da shiri ga matasan in sun kammala. Akwai kamfanoni masu zaman kansu da za su dauke su aiki da zarar sun kammala.''

Karin Bayani: Dubban matasa za su rasa aiki a Najeriya

Alummar  Najeriyar dai na cike da fata ta samun Karin kafar sama masu aiyyukan yi da  ake danganta hali na rashin tsaro da kasar ke fuskanta da hali na rashin aikin yi da taluci da ya kara jefa alummar kasar cikin rukuni na ‘yan rabana ka wadatamu.