1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matsaloli da sababbin buruka

August 27, 2020

Bayan share tsawon lokaci tana ta jan kafa, Tarayyar Najeriya ta kama hanyar komawa ga zamani inda amincewa da sayo na'urori na zamanin dama kari na makamai domin tunkarar matsalar rashin tsaro a kasar.

https://p.dw.com/p/3hbBp
Nigeria Präsident Mohammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Kama daga jiragen da ke tuka kansu ya zuwa ragowar na'urori na zamani dai, Najeriyar ta ce tana shirin kara yawa na makamai da jami'an tsaron kasar ke da bukata da nufin kai karshen matsalar 'yan ta'adda. A fadar mashawarcin gwamnatin kasar kan al'amuran tsaro Janar Babagana Monguno ana shirin kafa wata  cibiyar gano wa tare da karbe kananan makamai daga hannun 'yan kasar da toshe haanyoyin da suke kwararar Najeriyar.

Mongunon dai ya shaidawa taron majalisar magabata ta kasar na farko cikin tsawon shekara guda da rabi a Abuja, cewar Najeriya ta yi nisa a kokarin daukar matakai a zamanance da nufin mayar da matsalar tsaron da ta addabi sarakuna da ma talakawa, ya zuwa batu na tarihi a lokaci kankani.
An dai dauki lokaci ana  takkadama kan yadda kasar ta kashe  miliyoyin kudi amma ta kare da makamai marasa inganci, abin kuma da ke zaman guda cikin hujjojjin da ake ta'allakawa da rashin nasarar yakin na ta'adda da ma 'yan ina da kisan da ke kara mamaye sassa na kasar.

Nigeria Soldaten des Tschad patrouillieren in Monguno
Sayen kayan yaki ga sojojiHoto: AFP/A. Marte

Fargabar fadawa karancin cimaka biyo bayan ta'azzarar matsalolin tsaro a arewacin Najeriya

To sai dai kuma har ya zuwa yanzu, batun na kara makamai maimakon sake dabara na zaman na kan gaba a tunanin masu mulkin na Abuja. Sanata Ahmed Lawal na zaman shugaban majalisar dattawa ta kasar kuma daya a cikin mahalarta taron, a cewarsa kasar ba ta da zabin da ya wuce ci gaba a cikin zuba jarin na makamai da nufin tunkarar annobar da ta kai ga su kansu 'yan ina da kisan biyan danyen zinari a Zamfara, domin sayen makamin yaki da jami'an tsaron Najeriyar.

Nigeria Viehdiebstähle in ländlichen Regionen
Yawaitar kananan makamaiHoto: DW/Katrin Gänsler

Batun rashin tsaron dai na zaman guda a cikin wasu sababbin manufofi guda tara da shugaban kasar ya ce yana fata ya cika a shekaru ukun da ke tafe, duk da talaucin da kasar take ciki sakamakon COVID-19. Ko bayan aikin yi da yakin hanci da batun na tsaro da Abujar ta ambata tun daga farkon fari dai, Abujar ta kuma kara da batu na lafiya da inganta ilimi da mulki na gari, duk a cikin sababbin burikan da gwamnatin ta Shugaba Muhammadu Buhari take neman ta cika a ragowar shekaru ukun da ke tafe.

Najeriya: Mallakar bindiga domin kariya

A fadar malam Garba Shehu da ke zaman kakakin gwamnatin, akwai fatan nasara duk da rashin kudin da ke gaban mahukuntan yanzu. Najeriyar dai na tsaka a cikin tsallen murnar samun nasarar rage tasirin COVID-19 ga batu na tattali na arzikin kasar da ya kara karfafa gwiwar 'yan mulki na kasar.