1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin shawo kan tsiyacewar Najeriya

Ubale MusaSeptember 22, 2016

Hukumomi a Abuja na can na ganadawa don kokarin shawo kan rugujewar tattalin arziki da kasar ke fama da shi, inda ake bada rahotannin yadda jama'a ke fiskantar tsananin rayuwa

https://p.dw.com/p/1K6ie
Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident
Hoto: Reuters/A.Sotunde

A ci-gaba da kokarin neman mafita a cikin rikicin tattalin arzikin Tarayyar Najeriya, majalisar tattalin arzikin kasar na gudanar da taronta na farko tun bayan tabbatar da masassarar da ta shake tattalin arzikin cikin watan jiya.

'Yan majalisar da suka kunshi gwamnonin kasar 36 da sauran masu ruwa da tsaki kan batu na tattali na arziki dai, na nazarin dabarun da gwamnatin kasar ke dauka da nufin ficewa a cikin matsalar da ke zaman irinta mafi kamari a shekaru kusan 30 baya.

Ko bayan kisan kudi kamar ba gobe dai, gwamnatin na kuma tunanin cefanar da kaddarori na gwamnati dama samun bashi na kasashe na waje, da nufin sake ginin imani bisa tattalin arzikin da ya sha kashi.

Matakan kuma da mahukuntan na Abuja ke fatan na iya kaiwa ga sake ginin tattalin arzikin kafin karshen bana.