1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman sasantawa a kasar Burundi

Salissou BoukariJuly 15, 2015

Shugaba Museveni na Yuganda ke shiga tsakani a kokarin gano bakin zaren warware rikicin siyasar Burundi.

https://p.dw.com/p/1Fz8j
Uganda Präsident Yoweri Museveni
Hoto: Getty Images/AFP/D. Hayduk

Batun tattaunawa a kwanaki na biyu kuma na karshe da shugaban kasar Yuganda Yoweri Museveni ke jagoranta a kasar Burundi tare da bangarorin kasar, a wani mataki na samun mafita kan rikicin da Burundin ke fama da shi, na fuskantar babban tarnaki. Hakan dai ya zo a daidai lokacin da bangaren 'yan adawar kasar suka kafe a kan bakansu na cewa, ba su yarda da takarar shugaba Pierre Nkurunziza ba a wa'adi na uku, yayin kuma da ya rage kasa da mako guda da zaben shugaban kasa a Burundin.

Yoweri Museveni wanda kungiyar kasashen yankin Gabashin Afirka ta nada ya shiga tsakanin domin neman ceto kasar ta Burundi da ke daf da fadawa cikin yakin basasa, ya fice daga kasar, ba tare kuma da ya yi bayani kan sakamakon tattaunawar da ya yi da bangarorin kasar ba.

Tattaunawa kan batutuwa da dama

Sai dai ya ce bangarorin sun amince su tattauna da juna kuma bisa kowane fanni na rikicin tare da ba da tabbacin cewa ba za su katse tattaunawar ba har sai an kai ga samun mafita.

Burundi Militärputsch gescheitert
Magoya bayan Nkurunziza bayan juyin mulkin da bai yi nasara ba cikin watan MayuHoto: Reuters/G. Tomasevic

Museveni dai ya damka batun ci gaban tattaunawar a hannun ministansa na tsaro Crispus Kiyonga, wanda ake sa ran zai ci gaba da tattaunawar daga ranar Alhamis. Sai dai tun da farkon soma wannan tattaunawa ne, Museveni ya yi jan hankali ga bangarorin kasar.

''Idan ya kasance a kowane lokaci kowa zai rinka daukan kanshi shi dan wannan kabila ne ko na wancan, da misali ya ce ni dan Hutu ko dan Tutsi ne, to ku sani cewa wannan kasa ba za ta taba samun cigaba ba. Idan ya kasance kuna tare kuma kuka hada karfinku to dole ne kasar Bunrundi ta yi karfi ta bunkasa, amma idan ya kasance ‘yan siyasar kasar na da akida irin wadda suke da ita yanzu na kullum rikici, to kasar Burundi, ko Yuganda, ko kuma Ruwanda ba za su taba zama kamar misali Korea ta Kudu ba.''

Har yanzu dai ba a samu tudun dafawa ba

'Yan adawar kasar ta Burundi dai sun nemi mai shiga tsakanin, wanda kuma ya zamo mai shaida a yerjejeniyar birnin Arusha da aka yi a shekara ta 2000 da ya dawo kan shawarwari da kuma tsarin da kungiyar Tarayyar Afirka ta yi don samun mafita ga wannan rikici. Sun nace a kan bakansu na cewa sai an tattauna har ma da batun tsayawa takarar shugaba Nkurunziza da kuma batun tsayar da lokacin zaben da kowa zai yi na'am da shi. Domicien Ndayieze tsofon shugaban kasa ne kuma daya daga cikin jagororin 'yan adawar kasar ta Burundi.

"Idan har ba za mu yi kokarin daukan matakan da suka dace ba, to akwai hadarin wannan kasa tamu ta Burundi za ta fada cikin yakin basasa. Kuma na yaba da kalaman shugaban Yuganda Yuweri Museveni inda a jawabinsa na farko ya ce mu yi hankali da akidar bangaranci, domin bangaranci a nan wajajanmu kamar kabilanci ne, wanda kuma mun san irin miyagun illolin da hakan yake da shi tun lokacin da muka samu mulkin kai.''

Burundi Proteste gegen Präsident Nkurunziza Demonstration
Zanga-zangar adawa da Nkurunziza a birnin BujumburaHoto: Getty Images/AFP/J. Huxta

Bisa dukkan alamu dai ci gaban wannan tattaunawa zai kasance batu mai babbar sarkakiya yayin da gwamantin ta Burundi ke nanata cewa, ta yi duk abin da ya dace na ganin an samu sasanta wannan matsala. Aime-Alain Nyamitwe shi ne ministan hulda da kasashen waje na kasar ta Burundi.

''Gwamnati dai ta yi iyakar kokarinta na nuna aniya mai kyau, inda ta yi amfani da wasu shawarwari da aka bayar kamar misali kwance damarar duk matasan da ke dauke da makamai, da batun sake duba lokacin zabe. Kuma gwamnati a shirye take ta sassauto sosai don ganin an samu jittuwa, amma kuma dokokin kasar ne da kansu suka yi wa gwamnatin shamaki.''

A halin yanzu dai ana iya cewa wannan ita ce dama ta karshe da ta rage wa kasar ta Burundi da 'yan kasar baki daya na ganin sun aminta kan abun da zai fitar da kasar daga fadawa cikin wani sabon yanayi na yake-yake, ganin yadda a daren ranar Talata ma, an yi ta jin karan fashewar gurneti, tare da manyan bindigogi a wasu unguwanni na masu adawa da tsarin shugaba Nkurunziza duk kuwa da cewa ana zaman sasantawar.