1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da Muhalli

Kokowa da kalubalen sauyin yanayi a duniya

November 17, 2016

Taron MDD kan sauyin yanayi a duniya na COP22 na birnin Marrakesh na Maroko ya jaddada bukatar karfafa yarjejeniyar birnin Paris ta COP21 da ta tanadi rage dumamar yanayi da digiri daya da rabi zuwa biyu.

https://p.dw.com/p/2Spu8
Umweltprojekt-Trinkwasser aus Nebel in Marokko
Hoto: DW/M. Akinou

Taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP22 na birnin Marrakesh na Maroko na a matsayin wata amsa ga sabon shugaban Amirka Donald Trump wanda a lokacin yakin neman zabensa ya bayyana adawarsa da yarjejeniyar COP21 ta birnin Paris. A daidai lokacin da kasashen duniya ke wannan taro tashar DW ta gabatar da rahotanni kan yadda matsalar sauyin yanayi ta kasance a wasu kasashen nahiyar Afirka.