1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koma baya kan warware rikicin Siriya

May 1, 2013

Rahotannin na nuna cewar jakada na musamman na Majalisar Dinkin Duniya da kasashen larabawa kan rikicin Siriya Lakhdar Brahimi na shirin yin murabus daga mukaminsa.

https://p.dw.com/p/18QGA
Lakhdar Brahimi, Joint Special Representative of the United Nations and the League of Arab States on Syria, arrives to attend the Munich Security Conference on February 1, 2013 in Munich, southern Germany. High-level officials, ministers and top military brass gathered at the Munich Security Conference Friday with Syria in the spotlight and amid a US warning to Iran over stalled nuclear talks. AFP PHOTO / THOMAS KIENZLE (Photo credit should read THOMAS KIENZLE/AFP/Getty Images)
Lakhdar Brahimi auf der Münchener SicherheitskonferenzHoto: Getty Images

Guda daga cikin jakadun kasashen labarawa a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ne ya tabbatar da hakan a wata hira da yi da kamfanin dillacin labarai na AFP inda ya ce Mr. Brahimi ya shaida mu su cewar zai yi murabus kasancewar babu alamar kaiwa ga warware rikicin kasar duba da yadda kan kasashen duniya ya rabu dangane da rikicin.

Baya ga wannan matsalar a hannu guda 'yan tawayen na Siriya sun zargi Brahimi da gaza yin daidaito wajen warware rikicin yayin da gwmantin Assad a nata bangaren a makon da ya gabata ta ce ba za ta sake tattaunawa da shi ba dangane da sasasanta bangarorin biyu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar