1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta nuna goyon baya ga Donald Trump

Mohammad Nasiru AwalJune 1, 2016

Jaridar gwamnatin Pyongyang ta kwatanta Trump da dan siyasa mai basira da hangen nesa da zai ceto Amirka daga barazanar makaman nukiliya.

https://p.dw.com/p/1IyUV
USA Vorwahlen Kandidat Donald Trump
Hoto: Reuters/J. Skipper

Mai neman tsayawa takarar neman shugabancin Amirka karkashin jam'iyyar Republicans Donald Trump ya samu goyon baya daga mahukuntan Koriya ta Arewa. Jaridar gwamnati a birnin Pyongyang ta yaba wa dan jam'iyyar Republican din da zama wani dan siyasa mai basira da kuma hangen nesa da zai iya ceto Amirka daga barazanar makaman nukiliya. Da farko dai a cikin watan hira Trump ya ce a shirye yake ya tattauna da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un a kan shirin makaman nukiliyar kasar mai bin tsarin Kwaminisanci. Kasar ta kuma yaba da shawarar da Trump din ya bayar na janye dakarun Amirka daga Koriya ta Kudu. Sai dai jaridar ta Koriya ta Arewa ta caccaki Hillary Clinton da ke neman tsaya wa jam'iyyar Demokrat takara da cewa dakikiya ce kasancewa ra'ayinta ya saba da na Trump dangane da Koriya ta Arewa.