1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Kudu: Moon Jae-In ya lashe zabe

Gazali Abdou Tasawa
May 9, 2017

Rahotanni daga Koriya ta Kudu na cewa Moon Jae-In ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a wannan Talata a kasar bayan da ya samu kashi 41,1% na kuri'un da aka kada.

https://p.dw.com/p/2cgkc
Südkorea Präsidentschaftswahlen Moon Jae-in
Hoto: Reuters/Kim Hong-Ji

Rahotanni daga Koriya ta Kudu na cewa Moon Jae-In ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a wannan Talata a kasar bayan da ya samu kashi 41,1% na kuri'un da aka kada.

Koriya ta Kudu ta shirya wannan zaben gaba da wa'adi ne bayan da aka  tsige tsohuwar shugabar kasar Park Geun Hye a sakamakon wata badakalar cin hanci da aka bankado a gwamnatin tata. Mutane sama da kashi 75% na wadanda suka cancanci zaben ne suka fito suka kada kuri'arsu inda da dayawa daga cikinsu suka yi amfani da wannan dama domin huce hushinsu kan 'yan siyasar kasar da suka yi kaurin suna wajen cin hanci. 

Babban kalubalanen da ke a gaban sabon shugaban dai sune na matsalar tsadar rayuwa da rashin aikin yi da ake fama da su a kasar.