1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Isra'ila ta yanke hukunci ga sojinta

Yusuf Bala Nayaya
January 4, 2017

An dai gano bidiyon Sajant Elor Azaria na harbi a goshi ga wani Bafalatsine da ba makami a hannunsa wanda ake zargi da kai hari da wuka.

https://p.dw.com/p/2VHCH
Israel Tel Aviv Prozess Elor Azaria
Hoto: Reuters/H. Levine

Kotun soji a Isra'ila ta yanke hukuncin aikata kisa ba da gan-gan ba ga wani sojin kasar bayan da ya harbe har lahira wani dan Falasdinu wanda ba ya dauke da makami, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku ce a kasar tsawon watanni tara da ya raba kawunan 'yan kasar.

A hukuncin da ba kasafai ake ganin irinsa ba, kotun ta sami sojan da amfani da makami ba bisa ka'ida ba, abin da ake ganin zai kara dagula lamura. An dai gano bidiyon Sajant Elor Azaria na harbi a goshi ga wani Bafalatsine da ba makami a hannunsa wanda ake zargi da kai hari da wuka a watan Maris a yankin Hebron a Yamma da Kogin Jodan.

Kwamandojin sojin na Isra'ila dai sun nuna rashin jin dadinsu da matakin da sojan ya dauka yayin da wasu da yawa cikin al'umma da kawancen jam'iyya mai mulki ke tare da shi. Kanal Maya Heller,da ta yanke hukuncin ta ce sojan da lauyan da ke kare shi sun gaza bada shedu na kasancewar Bafalatsinen barazana sai dai Elor ya har be shi saboda kawai ya na ganin ya cancanci mutuwa ne.