1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Masar na zargin Mohammed Morsi da laifin cin amanar ƙasa

September 6, 2014

Kotun na tuhumar tsohon shugaban ƙasar tare da wasu muƙarabansa da laifin ba da wasu bayyanai na siri da suka shafi tsaron ƙasa ga ƙasar Qatar.

https://p.dw.com/p/1D88u
Mohammed Mursi
Hoto: STR/AFP/Getty Images

A lokacin da ya bayyana a gaban alƙalin da ke yin bincike domin ammsa tambayoyi. Morsi ya ƙi ya ce komai dagane da zargin kana kuma ya ci gaba da cewar shi ne har yanzu shugaban ƙasar na Masar.

Wata sanarwa kotun ta ce nan gaba za a yi masa shari'a a kan wannan tuhuma wacce ake zarginsa da ba da wasu bayyanan gwamnatin ga gidan telbijan na Al-Jazeera tare da karɓar wasu maƙudan kuɗaɗe. Daga cikin waɗanda ake zargi har'da wani na hannun daman tsohon shugaban Amine El Serrafi da kuma wani ɗan jaridar na Al-Jazeera. Tsohon shugaban na Masar na fuskantar tuhuma guda uku a ciki har'da ta leƙen asiri da haɗin baki da Ƙungiyar Hamas.

Mawalafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman