1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Nigeria ta yanke hukunci daurin watani 6 ga turawan da ka samu da leffin samogar din Man petur

December 14, 2005
https://p.dw.com/p/BvGQ

A taraya Nigeria, kotu ta yanke hukunci daurin watani 6, ga wasu matuka jirgin ruwa 15, da su ka hada da rashawa 12, da yan Georjia 2, da kuma daya na Ukraine.

Wannan turawa da a ka tsare tu shekara ta 2003, an same su da leffikan samogar din danyan man petur, da a ka sato daga yankin Niger Delta.

Jirgin ruwan da a ka kama su, na tukawa na dauke da tonne 11. 300 na dayan petur, da kudin su ya tashi kimanin Euro million 2.

Alkalin da ya yi shari´ar ya sannar cewa hukunci daurin, ya fara tun daga lokacin da a ka kama su, ma´ana, za su iya fita daga kurkuku kasancewa sun riga sun share fiye da shekaru 2 a ciki.

Tun shekara da ta gabata, a ka fara wannan shari´a, wadda a sakamakon jinkirin da a ka fuskanta, hukumomin Rasha, su ka nuna rashin gamsuwa ga takwarorin su na Nigeria.

Idan ba a manta ba, jirgin ruwan,da a ka yi samogar da shi ne, a ka bada sanarwar cewa, yayi kasa ko bisa a shekara da ta gabata,alhali kuwa,akwai jami´an tsaro na mussaman, da a ka azawa yaunin kulla da shi.