1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Spain ta dakatar da zaɓen Kataloniya

Abdourahamane HassaneSeptember 30, 2014

Babbar kotun tsarin mulki ta ƙasar Spain ta zartas da hukuncin dakatar da zaɓen raba gardama a kan Yankin Kataloniya na ƙasar da ke ƙoƙarin ɓalewa.

https://p.dw.com/p/1DNRZ
Barcelona Demos pro und kontra Unabhängigkeit 11.09.2014
Hoto: Josep Lago/AFP/Getty Images

Alƙalan kotun baki ɗaya suka amince da buƙatar da gwamatin ta Spain ta shigar na dakatar da ƙuria'r ta jin ra'ayoyin jama'a,wacce za ta yi aiki har tsawon watannin biyar kafin kotun ta tanttance ko za ta tsawaita ko kuma ta soke dakatarwar.

Firaministan na Spain Mariano Rajoy ya ce yin ƙuri'ar raba gardamar wani abu ne da ya saɓama kudin tsarin muli na ƙasar. Nan gaba ne majalisar dokokin ƙasar ta Spain za ta tattauna batun.