1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta amince da jinkirta zaben Kwango

October 18, 2016

Kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango ta amince da bukatar hukumar zabe na jinkirta zaben kasar har zuwa shekara ta 2018.

https://p.dw.com/p/2RMHt
Italien Vatikan Kabila beim Papst
Hoto: picture alliance/ZUMAPress/Evandroinetti

Kotun tsarin mulkin kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango ta amince da bukatar hukumar zaben kasar kan jinkirta zabe. Ita dai hukumar zaben ta tsaya kai da fata tana bukutar lokaci domin sabunta sunayen masu zabe.

Wannan matakin ya nuna cewa ba za a gudanar da zabukan shugaban kasa, da 'yan majalisa, gami da yankuna ba har sai zuwa watan Afrilu na shekara ta 2018. Bisa tsarin mulki wa'adin Shugaba Joseph Kabila yana kawo karshe a watan Disamba mai zuwa.