1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta ba da umarni Zakzaky ya ga likitansa

Yusuf Bala Nayaya
January 22, 2019

Wata kotu a Najeriya ta ba da umarni ga hukumar tsaron farin kaya a kasar ta ba da dama ga malamin nan da ke samun goyon bayan kasar Iran ya je ya ga likitansa yayin da lamarin lafiyar malamin ke ci gaba da tabarbarewa.

https://p.dw.com/p/3BzRw
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

Ibrahim Zakzaky da ke zama malamin 'yan  kungiyar 'yan uwa Musulmi karkashin kungiyarsu ta IMN, hukumar tsaron farin kayan na rike da shi tun daga watan Disamba na shekarar 2015

An dai kama shi a lokacin da jami'an tsaron Najeriya suka kaddamar da kame-kamen 'yan Shi'a a garin Zariya da ke arewacin Najeriya, inda dakarun suka halaka 'yan Shi'ar 300 kana suka binne su a katon kabari guda.

Lauyan da ke kare Zakzaky Maxwell Kyon, ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa sun nemi kotun ta ba da dama ga likitan da ke duba malamin ya duba shi, saboda rashin kulawar da ta dace da suke gani a hannun jami'an na DSS.