An daure tsohuwar shugabar Koriya ta Kudu
July 20, 2018Talla
An sami Park mai shekaru sittin da shida da haihuwa da laifin janyo wa kasa asarar dukiya da kuma yin katsalandan a harkokin zaben kasar na 2016. A can baya wata kotu ta yanke mata hukuncin dauri na shekaru ashirin da hudu bisa zargin cin hanci da rashawa da ya janyo wa gwamnatin asarar fiye da dala miliyan ashirin da shida. Misis Park ta musanta duk wadannan zarge-zargen baki dayansu.