1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure 'yan tawayen Ruwanda biyu

Mouhamadou Awal BalarabeSeptember 28, 2015

Kotun tarayyar Jamus ta samu wasu tsaffin shugabannin 'yan tawayen FDLR biyu da hannu a kashe-kashe ba gayra da ke wakana a Jamhukiyar Demokaradiyar Kwango

https://p.dw.com/p/1Gelo
Deutschland Prozess gegen mutmaßliche Kriegsverbrecher der ruandischen Rebellenorganisation FDLR
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Calagan

Wata kotun birnin Stuttgart ta Jamus ta yanke wa wasu tsaffin 'yan tawayen Ruwanda biyu hukuncin daurin shekaru 13 da kuma takwas a gidan yari, bayan da ta same su da laifin kisan kiyashi a Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango. Shekaru hudu wannan kotu ta shafe tana gudanar da wannan shari'a kafin ta daure tsaffin shugabannin kungiyar tawaye ta FDLR wato Ignace Murwanashyaka da kuma Straton Musoni.

Babban mai shigar da kara ya nemi a yanke musu hukuncin daurin rai da rai ne. Sai dai kuma alkali ya yi watsi da zarge-zarge 13 daga cikin 39 da aka yi kafin ya yanke hukunci. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon ya yaba matakin da Jamus ta dauka na gurfanar da 'yan tawayen biyu gaban kuliya.

Tun dai shekaru 10 da suka gabata ne Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasar Ruwanda suke neman 'yan tayen biyu bisan hannu da suke da shi a rikicin gabashin kwango Demokaradiya da ya ki ci ya ki cinyewa.