1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta tuhumi Musharraf

Usman ShehuAugust 20, 2013

A ƙasar Pakistan an samu tsohon shugaban ƙasar janar Pervez Musharraf da aikata laifi

https://p.dw.com/p/19TjH
Former Pakistani president Pervez Musharraf (C) is escorted by soldiers as he salutes on his arrival at an anti-terrorism court in Islamabad on April 20, 2013. A Pakistani anti-terrorism court on April 20 extended former military ruler Pervez Musharraf judicial remand to prison for two weeks for sacking judges during his rule, officials said. AFP PHOTO / AAMIR QURESHI (Photo credit should read AAMIR QURESHI/AFP/Getty Images)
Pervez Musharraf a gaban kotuHoto: AAMIR QURESHI/AFP/Getty Images

Jam'iyyar tsohon shugaban ƙasar Pakistan janar Pervez Musharraf ta yi watsi da hukuncin da wata kotu ta yanke na cewa Musharraf yana da hannu a kisan tsohuwar firimiyar ƙasar Benazir Bhutto. Kakakin jam'iyyar Musharraf, yace sun kaɗu da hukuncin kotun, ya ci-gaba da cewa ta yaya za'a ce shugaban ƙasa yana da hannu a kisan wani, don lamarin ya faru a mulkinsa kawai? don haka a faɗar kakakin jam'iyar janar Musharraf, wannan tuhumar shiri ne kawai. Kotu a ƙasar ta Pakistan dai, ta bayyana cewa janar Musharraf na da laifi, domin yaƙi baiwa Benazir Bhutto kariya ta jami'an tsaro yadda ya kamata, don haka za a yanke masa hukunci. Har yanzu dai akwai wasu laifukan da kotu ke tuhumar Muasharraf da aikatawa, waɗanda suma ba a kai ga cewa ko ya aikta ko a'a. Amma dai ko ba komai, masana suka ce wannan shine karo na farko da aka yankewa wani tsohon shugaban ƙasar Pakistan hukuncin aikta lafi, a ƙasar wanda tun samun yancin kai a shekara ta 1947, kusan duk sojoji ne ke mulkinta.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mouhamad Awal Balarabe