1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Burkina Faso ta bada sammacin Guillaume Soro

Salissou BoukariJanuary 15, 2016

A wani mataki na neman sanin hasken lamarin abun da ya wakana ga juyin mulkin da bai yi nasara ba a Burkina Faso, kotu a kasar ta bada sammacin kamo mata Guillaume Soro.

https://p.dw.com/p/1HeSO
Guillaume Soro
Guillaume SoroHoto: DPA

Kotun ta Burkina Faso, ta bada sammacin Guillaume Soro da ke a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar Cote d'Ivoir a halin yanzu kuma tsofon madugun 'yan tawayan Arewacin kasar. Shugaban kasar ta Cote d'Ivoir Alassane Ouattara, da na Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré, a baya-bayannan sun yi kokarin ganin sun daidaita huldar da ke tsakanin kasashen biyu, sai dai ana ganin wannan mataki da kotun ta Burkina Faso ta dauka, zai haifar da babban tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu da ke da babbar alaka a fannoni da dama.

Wata majiya ta ma'aikatar shari'ar kasar ta Burkina Faso, ta ce an bada sammacin kamo Soro din ne a binciken da ake kan juyin mulkin da bai yi nasara ba na ranar 17 ga watan Satumba da ya gabata, inda ake zargin mista Soro da hannu wajan kitsa tayar da zaune tsaye a kasar ta Cote d'Ivoir.