1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Habasha taki amincewa da belin abokan adawa

Hauwa Abubakar AjejeJanuary 4, 2006

A yau babbar kotun kasar Habasha,ta ki amincewa ta bada belin shugabannin adawa da yan jarida su 131,wadanda take tuhuma da laifin cin amanar kasa da wasu laifuka da suka shafi yunkurin hambarar da gwamnatin kasar bayan zabe da ake tababa a kansa.

https://p.dw.com/p/Bu2j
Hoto: AP

Alkalin babbar kotun ta Habasha,Adil Ahmed yace,laifukan da ake tuhumar yan adawan da su manyan laifuka ne, ta yadda ba damar a bada belinsu a halin yanzu,kana ya dakatar da sauraron shariar zuwa wata mai zuwa domin basu damar tuntubar lauyoyinsu.

Wadannan mutane sun hada da kusan dukkan shugabannin jamiyar adawa ta CUD da wasu yan jarida 22,wadanda suka ki amincewa su amsa laifuka da ake tuhumar su,wadanda suka hada da,cin amanar kasa,yunkurin juyin mulki da kisan gilla.

Tun farko dai yan adawan sun koka da rashin basu iznin tuntubar lauyoyinsu tun lokacinda aka tsare su a watan nuwamba,bayan zanga zangar kin amincewa da sakamakon zaben ranar 15 ga watan mayu,wadda abokan adawa suka ce an tafka magudi cikinsa.

Wani babban jamiin jamiyar ta CUD,Berhanga Nega,yace,idan kotu bata shirya jin koke koken mu ba,to bama so ta ci gaba da sauraron wannan sharia.

Alkalin ana shi bangare yace,zasu sauraresu ne kadai idan sun amsa wasu tambayoyi kokuma sun amince da laifukan da ake tuhumarsu akai,yace koma bayan haka kotu bata da lokacin da zata saurari batutuwa da basu da muhimmanci ga shariar,ya kara da cewa kotu ba wurin kanfen siyasa ba ce.

Lauyoyi masu kare yan adawan sun nemi a bada belinsu,saboda a cewarsu, babu hujjar da kotu take da ita da zata kama su da wadannan laifuka,suka ce munafunci ne na siyasa kawai.

Kungiyoyi masu kare hakkin bil adama,da masu kare yancin aikin jarida da kuma masu bada gudumowa na kasa da kasa,sun yi watsi da wannan zargi,suna masu baiyana tsoronsu cewa,gwamnatin Prime minister Meles Zenawi,wadda ada take dasawa da Amurka,yanzu tana neman ja da baya daga alkawuranta bin tafarkin demokradiya.

A makon daya gabata dai,Kungiyar Taraiyar Turai tace tana shirin dakatar da miliyoyin daloli,na taimako ga kasar ta Habasha,saboda yadda yanayin siyasar kasar ya kasance a halin yanzu.

Shi dai Meles Zenawi,ya zargi shugabannin jamiyar adawa ta CUD da magoya bayansu da kokarin hambarar da gwamnatinsa inda yake cewa sun shirya zanga zangar kin amincewa da sakamakon zabe a ciki da wajen babban birnin kasar,Addis Ababa wanda yayi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 85 a watan yuni da nuwamban shekarar da ta gabata.

Jamiyar CUD a zaben, ta lashe kujeru 109 ne cikin kujeru 547 na majalisar dokokin kasar,amma tace ta kasa samun nasara ne saboda magudi da aka tafka a lokacin zaben,yanzu haka dai ta kauracewa majalisar tana mai kira ga talakawa da su ci gaba da zanga zanga domin matsawa gwamnati sake gudanar da zabe a kasar.