1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ICC na son bayanin Afirka ta Kudu kan al-Bashir

Yusuf BalaSeptember 7, 2015

Kotun ta birnin Hague ta ce mahukuntan na birnin Pretoria na da dama daga nan zuwa ranar biyar ga watan Oktoba su yi bayani kan rashin kama shugaban Sudan.

https://p.dw.com/p/1GSRQ
Omar al-Bashir in Sudan
Shugaba al-Bashir lokacin da ya je Afirka ta KuduHoto: picture-alliance/dpa/M. Ali

Kotun ICC da kan hukunta wadanda suka aikata manyan laifuka ta bukaci kasar Afirka ta Kudu ta yi bayani kan dalilan da ya sanya ta gaza kama shugaba Omar al-Bashir a watan Yuni lokacin da ya shiga kasarta duk kuwa da cewar mahukuntan kasar sun sani ya na da sammacen kasa da kasa da aka lika masa ne neman a mikashi ga kotun.

A wani umarni da kotun ta birnin Hague ta fitar a ranar Litinin din nan ta ce mahukuntan na birnin Pretoria na da dama daga nan zuwa ranar biyar ga watan Oktoba mai zuwa su bada bahasi kan dalilan rashin kamun na al-Bashir da ya halacci taron koli na kungiyar kasashen Afirka ta AU.

Kotun ta ICC dai na neman shugaba al-Bashir ruwa a jallo bisa zarginsa da laifukan yaki da take hakkin bil'Adama a rikicin yankin Dafur.