1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ICC za ta yi shari'ar harin Timbuktu

Abdul-raheem HassanAugust 22, 2016

A wannan Litinin ake fara shari'ar wani da ake tuhuma cikin wadanda suka kai hari a wuraren tarihi da ke birnin Timbuktu na kasar Mali.

https://p.dw.com/p/1JmeM
Mali Ahmad Al Faqi Al Mahdi vor dem Internationalen Strafgerichtshof in Den Haag
Hoto: Reuters/R. van Lonkhuisen

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya wato ICC da ke birnin The Hague na kasar Hololand, a wannan Litinin take bude zaman shari'a a kan mayakan jihadi da ake zargi da kai hari da ya rusa hubbaren waliyai a birnin Timbuktu na kasar Mali. Wannan wuri dai na zama daya daga cikin wuraren tarihi da ke karkashin kulawar kungiyar da raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO.

Ahmed al-Faqi al-Mahdi, mai kimanin shekaru 40, na cikin wadanda ake zargi da tarwatsa sanannen gidan tarihin. Wannan shari'a dai na zama sabon babi a tarihin kotun hukunta laifunkan yaki ta ICC, ganin shi ne karon farko da wani dan kungiyar jihadi ke gurfana a gaban ta.

A watan Afirilun shekara ta 2012 ne dai 'yan bindiga suka kaddamar da hari a birnin na Timbuktu da ya yi sanadiyar rugurguza wurare masu cike da dimbin tarihi.