Kotu kan yakin Yugoslaviya ta tabbatar da hukunci
April 8, 2015Kotun da ke hukunta masu laifukan yakin Yugoslaviya ta tabbatar da hukuncin daurin rai da rai da aka yi wa wani tsohon Janar na Bosniya Zdravko Tolimir, wanda yake da hannu a kisan kare dangin Srebnica na shekarar 1995, wanda ke zama laifi mafi muni da aka aiwatar a Turai tun bayan yakin duniya na biyu.
Tolimir dan shekaru 66 da haihuwa, an same shi da laifi a shekara ta 2012 bisa laifuka biyar da suka hada da kisan kare dangi, da hada baki domin kisan kare dangi, da kisan kai, da cin zarafin mutane bisa dalilan kabiloanci, abin da ya janyo aka daure shi tsawon rai da rai. Kuma bayan daukaka kara alkalin kotun da ke birnin Hague na kasar Netherland ya tabbatar da hukuncin. A shekara ta 2007 aka kama Zdravko Tolimir sai dai an samu tsaiko kan shari'ar bisa dalilan rashin lafiya.