1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Kenya ta soke matakin rufe sansanin Dadaab

Gazali Abdou Tasawa
February 9, 2017

Wata kotun kasar Kenya ta sanar a wannan Alhamis da soke matakin gwamnatin kasar na rufe sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da gwamnatin ta shirya za ta yi a watan Mayu mai zuwa.

https://p.dw.com/p/2XEzP
Kenia Flüchtlingslager Dadaab
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba


Wata kotun kasar Kenya ta sanar a wannan Alhamis da soke matakin gwamnatin kasar na rufe sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da gwamnatin ta shirya za ta yi a watan Mayu mai zuwa. Kotun ta ce matakin gwamnatin kasar ta Kenya na maida 'yan gudun hijirar Somaliya zuwa kasarsu ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Kusan ba zato ba tsammani ne dai a ranar shida ga watan Mayun shekarar bara gwamnatin kasar ta Kenya ta sanar da daukar matakin rufe sansanin na Dadaab wanda ke a matsayin sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya ba tare da shawarwata Kungiyoyin MDD masu aikin kula da 'yan gudun hijirar wanann sansani ba. 

Gwamnatin Kenya ta kafa hujjar daukar matakin ne a bisa a cewarta dalillai na tsaro tana mai zargin cewar daga wannan sansani ne aka kitsa harin ta'addancin da aka kai a cibiyar kasuwanci ta Wesgate ta birnin Nairobi a 2013 da kuma na jami'ar Garissa a 2015.